Northern TV

Northern TV News and Current affairs.
(1)

A cewar Sheikh Sani Yahaya Jingir, Ana cewa bamu da tsaro ko kaďan a Nijeriya, toh wannan maganar ba gaskiya ba ne, daga...
21/09/2026

A cewar Sheikh Sani Yahaya Jingir, Ana cewa bamu da tsaro ko kaďan a Nijeriya, toh wannan maganar ba gaskiya ba ne, daga Illela ana zuwa Fatakut dare da rana ana tafiya lafiya kalau.

21/09/2026

Shin ko Malam yayi gaskiya a maganan sa ?
Me ye ra'ayin ku?

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu.An ruwaito cewa Idris ya rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Sa...
20/09/2026

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu.

An ruwaito cewa Idris ya rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumbar 2026, a kasar Birtaniya yana da shekaru 77 a duniya.

Bayan rasuwarsa, Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo; tsohon Gwamna Yahaya Bello; Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Abdullahi Bello; da sauran manyan jami'an gwamnati sun ziyarci gidan marigayin da ke Abuja domin yi wa iyalansa ta'aziyya.

Onogwu Muhammed, wanda shi ne Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kogi kan Harkokin Sadarwa da Jama'a kuma Babban Sakataren Yada Labarai na tsohon Gwamna Yahaya Bello, ya bayyana labarin ziyarar ne a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, tare da hotunan Ododo da Bello a gidan.

Shugaba Bola Tinubu ya umurci dukkan gwamnonin jihohi 36 da su hanzarta aiwatar da Shirin Sufuri na Kasa Mai Sauƙi Mai A...
20/09/2026

Shugaba Bola Tinubu ya umurci dukkan gwamnonin jihohi 36 da su hanzarta aiwatar da Shirin Sufuri na Kasa Mai Sauƙi Mai Amfani da Iskar Gas (CNG) don tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun fara ganin raguwar farashin sufuri daga ranar 1 ga Oktoba.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a hukumance a ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, Shugaba Tinubu ya yi magana game da taronsa na ranar 27 ga Agusta da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), inda aka tsara wani haɗin gwiwa don rage farashin sufuri a faɗin ƙasar ta amfani da makamashin cikin gida.

20/09/2026

Yadda Gwamna Uba Sani ya bayyana ra'ayinsa cewar Shugaba Tinubu ne mafi cancanta ga Shugabancin Najeriya. Don babu wanda yakai shi kawoo cigaba kansar.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya soke mataimakinsa na musamman kan harkokin kafofin sad...
20/09/2026

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya soke mataimakinsa na musamman kan harkokin kafofin sada zumunta na zamani, Umar Alhassan (wanda aka fi sani da King Indara), saboda ya wallafa hoton da ke cewa "Abba Must Go"

Yayin da ya ke kare Bola Tinubu, Kahutu Rarara ya ce 'yan Najeriya sun yi kukan yunwa a baya, yanzu kuma sun dauko kukan...
20/09/2026

Yayin da ya ke kare Bola Tinubu, Kahutu Rarara ya ce 'yan Najeriya sun yi kukan yunwa a baya, yanzu kuma sun dauko kukan tsadar man fetur.

Wani jigo a jam’iyyar adawa ta ADC ya bayyana zarginsu da jam’iyyar keyi akan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shirin ...
20/09/2026

Wani jigo a jam’iyyar adawa ta ADC ya bayyana zarginsu da jam’iyyar keyi akan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shirin maido da tallafin man fetur don yaudaran talakawa. Sai kuma ya cire bayan ya ci zaɓe.

Hussaini Yusuf Datti na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben cike gurbi na Majalisar Jaha a mazabar ...
20/09/2026

Hussaini Yusuf Datti na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben cike gurbi na Majalisar Jaha a mazabar Dawakin Kudu/Warawa a jihar Kano da aka gudanar a ranar 19 ga Satumba, 2026.

19/09/2026

Yadda jihar Neja ta shige ruɗani bayan rasa rayukan matasa 37, sakamakon rufesu da jami'an Civil Defence s**a yi babisa ka'ida ba akan laifin hakar Zinari da suke ba a ka'ida ba.

Address

Broadcasting Corporation
Abuja
800283

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Northern TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category