16/06/2026
IRIN JAZBAR SHEHU MAJNUNU BARHAMA AL-KUSAWIY CIKIN SHEHI🤔
"
"
Shehu Abdurrazaq kusa ya ce: “Idan dã duka halitta Zata yiwa Allah laifi, Allah ya korosu Sai su zo bayan Shehu Abul Fathi Su fake, To idan SHEHI ya ce Allah a yi musu Afuwa, take Allah zai karbesu.“
Haka zalika ya kara cewa: “Idan dã Addini mutum ne idan ya yiwa Allah laifi mutum uku ne kawai zasu iya yin belinsa a wajen Allah, daya idan ya yi rubutu, dayan idan ya yi Magana, ya ce Amma Shehu Ahmadu yarwa wuyarta daya ya ji, da zarar maganar ta Shiga kunnensa ba sai ya ce komai ba Allah zai ce Bijaahika na yafe.”
Shehu Al-kusawiy ya sake cewa: “Na ga nadin waliyyai kala kala Amma tunda nake ban taba ganin Nadin waliyyin da Aka yi Shagali irin Shehu Ahmadu yarwa ba” Maganar gaiba ake ba Kuru Kuru ba.
Kuma haka nan Shehu Abdurrazaq kusa yana da ijazozi da yawa daga cikin Shehunnai Amma yana matukar Alfahari da ijazar da ya samu daga hannun SHEHI.
Ɗan Sayyida fadimatuz Zahra kenan🥰
✍️HUSSAINI AUTA53✨
✔️Futuhi Da'iman
✔️ 53 ba chanji