Apc Media Crew Zamfara State

Apc Media Crew Zamfara State news and current affairs department

09/07/2024

Shi ne ya nemo ma jahar zamfara lasisin mallakar jami'a ta kashin kanta.

Shi ne ya samar da filin da aka soma gina jami'ar bayan ya biya diyyar masu filaye.

Shi ne ya soma assasa ginin jami'ar, duk wanda ya zo sai dai ya dora a bayan sa.

Shi ne ya samar ma ta da mazauni na wucin gadi gabanin a kammala ma ta mazauni na dindindin.

Shi ne ya gina makarantun sakandare na sojojin sama (Command Secondary School) guda ukku, daya a Gusau, daya a Mafara sai daya a Kaura.

Shi ne ya gina cibiyar horar da malamai ta jaha (Teachers Training And Development Centre) domin horar da malammai sanin makamar aiki.

Shi ne ya biya diyar gidaje domin ginawa tare da fadada makarantar Islamiyya ta Zawiyyar Sheikh Balarabe, Gusau a karkashin tsarin Almajiri School.

Shi ne ya biya diyar gidaje tare da fadada makarantar Islamiyya ta Malam Abdulrahaman Jelani da ke Sabon Fegi, Gusau a karkashin tsarin Almajiri School.

Shi ne ya gina makarantar Islamiyya ta Sheikh Dalla Dalla da ke Mortgage, Gusau a karkashin tsarin Almajiri School.

Shi ne ya biya diyar gidaje tare da fadada makarantar Islamiyya ta Sarkin Malamman Mafara da ke Talatar Mafara a karkashin tsarin Almajiri School.

Shi ne ya gina katafariyar makarantun furamari na zamani guda biyu, wa'yan da babu irin su a yankin jahohin arewa maso yamma, daya a bayan hukumar UBE da ke Gusau, sai kuma daya a Talata Mafara.

Shi ne ya gyara kaso mafi tsoka na makarantun furamare a jahar zamfara.

Shi ne ya gyara kaso mafi tsoka na makarantun sakandare a jahar zamfara.

Shi ne ya nemo gurabu tare da daukar nauyin wasu matasan jahar zamfara zuwa jami'o'i biyu ma su zaman kansu a jahohin Kwara da Ogun.

Wannan tamkar amsa ce zuwa ga ma su s**ar shirin Tallafin HE Yari na daukar nauyin karatun matasan jahar zamfara su 1700 ta hanyar jefa tambaya cewa mi yassa bai yi irin haka inda aka fito ba, wasu kuma su ce mi ya yi ma ilimin jahar zamfara inda aka fito.

Ba da gudunmuwa akan ilimi bai takaita kadai akan biyan WAEC da NECO ba, bai takaita akan gina sabbin makarantu da gyara wa'yan da ke akwai kadai ba, bai takaita akan gyara albashin Malammai kadai ba, bai takaita akan baiwa dalibbai tallafin karatu kadai ba, fannona ne daban daban, duk fannin da Allah ya baiwa mutum dama ba laifi ba ne ya shagaltu da shi.

Duk abun da na fada a nan bai kai kashi 1/10 na kokarin da HE Yari ya yi ma ilimi a lokacin da Allah ya ba shi damar zama gwmanan jahar zamfara ba illa na dan tsakuro ne.

Duk da irin wannan namijin kokarin da ya yi ma bangaren ilimi, amma sunan shi makiyin cigaban ilimi a wurin wasu da son zuciya ya rinjayi son gaskiyar su.

Allah ya cigaba da yi ma sa jagoranci, ya kara ba shi juriya da hankuri.

Allah dawo muna da dauwamammen zaman lafiya a jahar mu da kasar mu baki daya.

IBG
09/07/2024.

SHARUƊƊAN BADA TALLAFIN KARATU GA ƊALIBBAI DUBU ƊAYA DA ƊARI BAKWAI (1,700) NA JIHAR ZAMFARA DAGA SANATA ABDUL'AZIZ YARI...
24/06/2024

SHARUƊƊAN BADA TALLAFIN KARATU GA ƊALIBBAI DUBU ƊAYA DA ƊARI BAKWAI (1,700) NA JIHAR ZAMFARA DAGA SANATA ABDUL'AZIZ YARI ABUBAKAR (SHATTIMAN ZAMFARA).

Wannan Kwamitin sun fitar da tsare-tsarin da suke buƙatar Ɗalibi ya cike kafin ya samu shiga cikin sahun Ɗalibai da za'a ba tallafin biyan Kuɗin Makaranta, kuɗin wurin kwana, Kayan aikin karatu dakuma Kuɗaɗe duk Wata domin gudanar da karatu yanda ya kamata.

Tsare-tsaren sune:
1) Ɗalibi ya samu gurbin Karatu a University dake Arewa maso Yamman Najeriya. (Anfi son haka)

2) Ɗalibi ya kasance tabbataccen Ɗan Jahar Zamfara kuma wanda baya da ƙarfin biyan kuɗin Makaratun Makaranta.

3) Ɗalibi ya kasance yana da takardun Shedar shi Ɗan Zamfarane kuma ya samu gurbi a cikin mutun 100 ko 150 daga Ƙaramar hukumarsa,

4) Ɗalibi ya samu gurbin karatu a ɗaya daga cikin Jami'o'in na Gwamnati. Ba'a ɗaukar nauyin wanda zaiyi karatu a Jami'oin kuɗɗi (Private Universities)

5) Za'a tantance Ɗalibban da s**a chanchanta ƙarkashin shugaban kwamitin Ƙaramar hukuma, wanda za'a fitar da Form a kowace ƙaramar hukuma.

6) An tanadi Hidikwatar karɓar ƙorafi ko hanzari daga Ɗalibban kowace ƙaramar hukuma a garin Gusau wanda yake daura da Huda University kan Hanyar zuwa Sokoto a Titin Byepass kafin NNPC Station.

Coordinators na L/Govt.
1- Engr. Babangida️️️ Abdullahi- Gusau
2- Dr. Al'amin Tsafe- Tsafe
3- Dr. Mansur Bello - Bunguɗu.
4- Prof. Yahaya Mafara - Maru.
5- Malam Aliyu Dan Madami - Maradun.
6- Prof Tukur Adamu - T/Mafara.
7- Dr. Abdullahi Maharazu - Bakura.
8- Alh Yusuf Monitoring Mafara - Anka
9- Sen Tijjani Yahaya- Kaura.
10- Sen Tijjani Yahaya- Shinkafi.
11- Barr Takori Gummi- Gummi.
12- Hon Ibrahim Dan Malikin Gidan Goga- Zurmi.
13- Hon Umar Jibo- Bukuyum.
14- Hon Muh'd Birnin Magaji- Birnin Magaji.

Muna rokon Allah madaukakin sarki ya shiga cikin wannan tsarin, Allah madaukakin sarki ya tabbatar da cikakkiyar nasara da galaba a cikin wannan tsarin, Allah madaukakin sarki ya saka ma Mai girma Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar da al’khairi irin na sa Amin.

09/10/2023

Wallahi mutane da dama na fama da rashin lafiya, ya ubangiji Allah wadanda basu da lfy na gida da asibiti, Allah kabasu lfy.

Address

No 12 Damba Area
Gusau

Telephone

+2347062973839

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Apc Media Crew Zamfara State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Apc Media Crew Zamfara State:

Share

Category