13/03/2024
MECECE BIDI'A A SHARI'A, KUMA SU WANENE 'YAN BIDI'A?
Tambaya:
"Ni har yanzu abun da ban gane ba shi ne WAi ita wannan bidi'ar wadda kake magana daga Ina ta fito ne?".
Amsa:
Ita wannar bidi'a da nake magana a kanta bayaninta ya fito ne daga Al- Qur'ani da Sunnar Annabi (saw).
Allah ne ya ce:
{أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ شَرَعُوا لَهُمْ مِنَ الدِّينِ مَا لَمْ يَأْذَنْ بِهِ اللَّهُ } [الشورى: 21]
"Ko suna da wasu abokan tarayya wa Allah ne da s**a shar'anta musu a Addini abin da Allah bai yi izini da shi ba?".
A cikin wannar ayar sai Allah ya muzanta masu masu shar'anta wasu abubuwa a Addini wadanda Allah bai yi izini ba, su da kuma masu binsu.
Annabi (saw) ya ce:
«أما بعد، فإن خير الحديث كتاب الله، وخير الهدى هدى محمد، وشر الأمور محدثاتها، وكل بدعة ضلالة»
صحيح مسلم (2/ 592)
"Bayan haka, lallai mafi alherin magana ita ce Littafin Allah, mafi alherin shiriya shiriyar Muhammand (Manzon Allah {saw}). Mafi sharrin lamura su ne fararrunsu, kuma kowace kirkirarriyar ibada (fararriya) bata ce".
Kuma ya ce:
«من أحدث في أمرنا هذا ما ليس فيه، فهو رد»
صحيح البخاري (3/ 184)، صحيح مسلم (3/ 1343)
"Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan lamari namu na Addini, abin da ba ya cikinsa to an mayar masa shi".
A wata riwayar ta Muslim:
«من عمل عملا ليس عليه أمرنا فهو رد»
صحيح مسلم (3/ 1343)
"Duk wanda ya aikata wani aiki wanda babu umurninmu a cikinsa to an mayar masa shi".
Saboda haka Addini shi ne abin da Allah ya yi izni ya shar'anta mana, Allah da Manzonsa s**a yi umurni da shi, wanda Manzonsa (saw) ya zo mana da shi a cikin Littafin Allah da Hadisansa (saw) ingantattu.
Shi ya sa duk abin da aka fare shi, wanda Allah da Manzonsa (saw) ba su yi umurni da shi ba, wanda ba ya cikin Qur'ani ko Sunna to wannan abin ba abin karba ba ne, saboda ba Addinin da Allah ya yi izni da shi ba ne, saboda bidi'a ne kirkirarriya, kuma dukkan bidi'a a Addini bata ce.
Saboda haka dukkan abin da ya saba wa Qur'ani da Sunna da Ijma'in magabata na Aqidu da Aiyuka na Ibada da Mu'amala bidi'a ne. Allah ba zai karba ba.
SU WANENE 'YAN BIDI'A?
Su ne wadanda s**a kirkiri abubuwa s**a shigar da su cikin Addini, alhali Allah bai shar'anta su ba, kuma shi da Manzonsa (saw) ba su yi umurni da su ba. Sawa'un a babin Aqida ne, ko kuma a babin Ibada ko mu'amala.
Misalan bidi'a a babin Aqida da Ibada su ne:
(1) Bidi'ar Asha'ira, sun saba wa Qur'ani da Sunna a babin Aqidun da Qur'ani da Sunna s**a zo da su, saboda suna daukan Addini ne daga hankali. Misali Allah ya fada a cikin Qur'ani cewa; yana Sama, ya daukaka a kan Al- Arshi, amma su kuma sun ce: a'a, yana ko'ina.
Allah ya ce:
{أَأَمِنْتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ أَنْ يَخْسِفَ بِكُمُ الْأَرْضَ فَإِذَا هِيَ تَمُورُ (16) أَمْ أَمِنْتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ أَنْ يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا } [الملك: 16، 17]
Allah ya ce: ya daukaka a kan Al- Arshi, nan ma sun ce: a'a.
Allah ya ce:
{الرَّحْمَنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى } [طه: 5]
Kuma sun kore sauran siffofin Allah masu yawa, in ban da 'yan kadan da suke tabbatar da su daga 7 zuwa 20 ba. Alhali siffofin Allah suna da matukar yawa, shi ne kawai ya san yawansu.
(2) Bidi'o'in Sufaye, wadanda suke daukan Addininsu daga Mafarkai da Zauqi da sauransu.
Suna da bidi'o'i masu yawa manya da kanana, daga ciki akwai:
1- Aqidar komai Allah ne.
2- Bauta a wajen kabarbura.
3- Zikirori da Wirdi da babu su a cikin Qur'ani da Sunna.
4- Maulidi.
(3) Bidi'o'in Rafidha 'Yan Shi'a, wadanda suke daukan Addini daga karerayin da s**a jingina wa Imamansu 12 ma'asumai. Su kam bidi'o'insu sun fi na kowa yawa, har yawansu ya sa s**a banbanta da sauran Musulmai a komai. Daga ciki:
1- Aqidarsu ta Imama, wacce take hukunta inkarin Khalifancin Abubakar (ra) da Umar (ra) da Usman (ra).
2- Aqidar Isma, -wai- ma'asumai su 14 ne, Annabi (saw) da Fatima (ra) da Imamansu 12, tun daga kan Aliyu (ra) har zuwa na karshensu Mahdinsu wanda suke zaton zai zo a nan gaba. Kuma saboda wannan ne suke guluwwi a game da su, har suke ba su wasu siffofi na Allah.
3- Aqidar kafirta Sahabbai ko s**ansu da aibantasu.
(4) Bidi'ar Khawarijawa masu fita daga cikin jama'ar Musulmai, suna halatta jinanensu, suna daukan makami a kansu suna kashesu, masu guluwwi da kafirta Musulmai ba tare da hujja ba, saboda rashin ilimi da jahiltar ma'anonin Qur'ani da Sunna, wadanda Manzon Allah (saw) ya ce a kansu:
يقتلون أهل الإسلام ويدعون أهل الأوثان
صحيح البخاري (4/ 137)، صحيح مسلم (2/ 741)
"Suna kashe masu bin Muslunci, suna barin masu bautar gumaka (kafirai)".
Ibnu Umar (ra) ya ce:
«إنهم انطلقوا إلى آيات نزلت في الكفار، فجعلوها على المؤمنين»
صحيح البخاري (9/ 16)
"Sun tafi zuwa ga ayoyin da s**a sauka a kan kafirai sai s**a sanyasu a kan muminai".
A takaice magana a kan bidi'a da 'yan bidi'a tana da yawa, wannan kawai a takaice ne.
Allah ya yi mana tsari gaba daya.
Saboda haka abin da yake wajibi a kan dukkan Musulmi shi ne riko da Mazhabar Ahlus Sunna wal Jama'a, wato hanyar riko da Qur'ani da Sunna a bisa fahimtar Sahabbai da Tabi'ai da Manyan Malaman Musulunci, irin su Imamu Malik, Shafi'iy, Ahmad da sauransu. Saboda su ne suke riko da Littafin Allah da Sunnar Manzonsa (saw), kuma suke girmamasu, kuma s**a fi kowa fahimtarsu, suke binsu suke daukan Addini daga garesu, a babin Aqida da Ibada da Mu'amala da Akhlaq da sauran abubuwa na Addini, sabanin wadancan 'yan bidi'a da muka ambata, ba sa girmama Qur'ani da Sunna, ba sa daukan Addini daga garesu, kawai suna dauka ne daga son ransu da mafarke - mafarkensu da ra'ayoyin shehunnansu da shugabanninsu.
Wallahu A'alam.
Allah ya shiryar da mu gaba daya.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani
3 Mar, 2015