14/09/2026
DA DUMI-DUMI: Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana muhimman manufofinsa guda 12 da ya ce zai aiwatar idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana manufofin ne a ƙarƙashin tsarin “Rescue, Revive and Restore Nigeria” — wato ceto, farfaɗo da dawo da martabar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan tattalin arziki, ilimi, tsaro, noma, wutar lantarki, lafiya da tsarin mulkin ƙananan hukumomi.
Ga muhimman manufofin da ya gabatar:
1. Mayar da tallafin man fetur:
Ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur da aka tsara, domin rage tsadar sufuri da kuma sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya matsin rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.
2. Sake duba bashin NELFUND:
Ya ce za a sake nazarin tsarin rancen kuɗin karatu na NELFUND, tare da duba yiwuwar afuwa ga wasu basuss**a, bisa hujjar cewa ɗaliban Najeriya sun cancanci tallafin karatu da ilimi mai sauƙin samu, ba bashin da zai jefa su cikin matsala ba.
3. Ƙarfafa cin gashin kan ƙananan hukumomi:
Atiku ya yi alkawarin aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan cin gashin kan ƙananan hukumomi, domin tabbatar da cewa kuɗaɗen da s**a dace da ƙananan hukumomi sun isa gare su kai tsaye kuma a yi amfani da su wajen ayyukan ci gaban al’umma.
4. Farfaɗo da tashoshin jiragen ruwa na Gabas:
Ya ce zai farfaɗo da haɓaka tashoshin jiragen ruwa na Port Harcourt, Calabar da Warri, tare da inganta ci gaban Uyo Deep Sea Port, domin ƙarfafa kasuwanci da sufuri ta teku.
5. Sake buɗe iyakokin ƙasa:
Ya yi alkawarin sake buɗe iyakokin Najeriya domin bunƙasa kasuwancin halal tsakanin ƙasashe, tallafa wa ‘yan kasuwa na gaskiya da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci a yankin.
6. Gyaran tsarin wutar lantarki:
Atiku ya ce zai sake duba tsarin bangaren wutar lantarki da kuma rabe-raben kuɗin wuta, domin kawo ƙarshen abin da ya kira cajin kuɗaɗen wuta cikin nuna bambanci da kuma rage wa ‘yan Najeriya tsadar wutar lantarki.
7. Tallafa wa matasa da mata:
Ya gabatar da shirin samar da dala biliyan 10 domin tallafa wa kamfanonin matasa da harkokin kasuwanci, tare da ƙara ba matasa da mata dama a nadin mukaman gwamnati da kuma fannonin tattalin arziki.
8. Ƙarfafa tsaron ƙasa:
Ya yi alkawarin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro, inganta jin daɗinsu, yaƙi da cin hanci a cikin hukumomin tsaro, amfani da sabbin fasahohin leƙen asiri da na aiki a filin daga, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen makwabta.
9. Mayar da ‘yan Najeriya gonaki:
Atiku ya ce zai inganta tsaron manoma, rage kuɗaɗen samar da amfanin gona, farfaɗo da harkar noma da kuma faɗaɗa hanyoyin samun tallafin kuɗi ga manoma da ‘yan kasuwa.
10. Gyaran harkar lafiya:
Ya yi alkawarin sake fasalin tsarin kiwon lafiya, faɗaɗa damar samun ingantacciyar lafiya mai sauƙin kuɗi, tare da magance ƙarancin ma’aikata, inganta albashi da kuma walwalar ma’aikatan lafiya.
11. Ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi iko:
Ya ce zai sake fasalin tsarin rabon iko tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi, ta hanyar duba Exclusive da Concurrent Legislative Lists, domin bai wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarin nauyi da damar gudanar da ayyukansu, yayin da gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali kan abubuwan da s**a shafi ƙasa baki ɗaya.
12. Aiwatar da Oronsaye Report:
Atiku ya ce zai aiwatar da shawarwarin Rahoton Oronsaye domin kawar da almubazzaranci, maimaita ayyuka tsakanin hukumomi da kuma rage guraben da ke haifar da cin hanci, tare da inganta ayyukan gwamnati da samar da ingantaccen tsarin gudanarwa.
Ya ce manufofin nasa sun kasance wani ɓangare na shirinsa na “ceto, farfaɗo da dawo da Najeriya” idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
KBC Hausa