Zauren_Makaranta

Zauren_Makaranta Dõmin karantarwa dã karawa junã ilmin Addini dã fahimtar Alkurani Mai Girma.

12/06/2026

NASIHA GA MASU KIRAN KANSU "MUHAMMADAWA"

Ya ku musulmai, ku ji tsoron Allah!

Allah Maɗaukakin Sarki bai kira mu Muhammadawa ba. Sunan da Allah Ya zaɓa mana shi ne Musulmi.

Allah Ya ce:

وَجَٰهِدُواْ فِي ٱللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِۦۚ هُوَ ٱجۡتَبَىٰكُمۡ وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمۡ إِبۡرَٰهِيمَۚ هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ مِن قَبۡلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيۡكُمۡ وَتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِۚ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعۡتَصِمُواْ بِٱللَّهِ هُوَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ فَنِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ.

"....Shi ne Ya sanya muku suna Musulmai tun farko da kuma a cikin wannan Alƙur'ani...." (Suratul Hajj: 78)

Don haka, me ya sa wasu suke barin sunan da Allah Ya zaɓa, su rungumi wani suna da ba Allah ne Ya ba su ba?

Annabi Muhammad (SAW) bai taɓa kiran mabiyansa "Muhammadawa" ba. Sahabbai ba su taɓa kiran kansu Muhammadawa ba. Tabi'ai da manyan malamai na farko ba su taɓa ɗaukar wannan suna ba. Idan da alheri ne, da su ne za su fara yin sa.

Wasu daga cikin masu adawa da Musulunci sun fi son kiran musulmai da sunan "Muhammadawa" maimakon "Musulmai". Dalili shi ne suna son Kalli Musulunci k**ar sauran addinai waɗanda ake danganta mabiyansu da sunan wani mutum. Kamar " Christ"
Watau "Christians" masu bin ko bautawa "Christ" annabi Isa Dan maryama.

Sai dai musulunci ba sa yarda da wannan fahimta.
Musulmai ba sa bauta wa Annabi Muhammad (SAW), kuma ba sa ɗaukarsa a matsayin abin bautawa.

Musulmai Mabiya ne ga saƙon da Allah Ya saukar masa. Saboda haka sunan da Allah Ya zaɓa musu shi ne Musulmi, ba "Muhammadawa" ba.

Asalin sunan al'ummar wannan addini daga Allah yake, ba daga sunan wani mutum ba.

Musulunci yana nufin miƙa kai ga Allah Shi Kaɗai, kuma Musulmi shi ne wanda ya miƙa kansa ga Allah.

Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne, bawan Allah ne, ba abin bauta ba ne. Mu mabiyan sa ne, amma addinin da muka zo da shi addinin Allah ne, ba addinin Muhammad ba.

Saboda haka sunan da ya dace da mu shi ne abin da Allah Ya sanya mana: Musulmi.
Duk wanda yake ƙoƙarin ɗaukaka wani suna sama da sunan Musulunci, to ya yi hattara. Domin yawaita laƙabobi da ƙungiyoyi na daga cikin abubuwan da s**a rarraba al'umma.

Don haka ya dace musulmi su yi alfahari da sunan da Allah Ya ba su, su gabatar da kansu a matsayin Musulmai, kuma su bayyana wa mutane cewa addininsu ba bautar Muhammad (SAW) ba ne, bautar Allah Shi Kaɗai ce.

Allah Ya ce:
..... وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ. مِنَ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُمۡ وَكَانُواْ شِيَعٗاۖ كُلُّ حِزۡبِۢ بِمَا لَدَيۡهِمۡ فَرِحُونَ .

"....Kuma kada ku kasance daga cikin mushrikai. Waɗanda s**a rarraba addininsu s**a zama ƙungiyoyi-ƙungiyoyi..." (Suratur Rum: 31-32)

Haka Kuma Allah Maɗaukaki Ya ce:
.... هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ مِن قَبۡلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيۡكُمۡ وَتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِۚ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعۡتَصِمُواْ بِٱللَّهِ هُوَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ فَنِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ.

"Shi ne Ya sanya muku suna Musulmai tun da farko da kuma a cikin wannan (Alƙur'ani)...."
(Suratul Hajj 22:78)

Wannan aya tana nuna cewa Allah ne Ya sanya wa mabiyan wannan addini suna "Musulmai", saboda haka shi ne sunan da ya k**ata a fi amfani da shi.

Saboda haka muna kira ga duk wanda yake amfani da sunan "Muhammadawa" da ya yi tunani cikin adalci: Shin wannan shi ne sunan da Allah Ya ba mu?
Shin wannan shi ne sunan da Annabi (SAW) ya koyar da sahabbansa?

Mu koma ga Alƙur'ani da Sunnah. Mu yi alfahari da sunan da Allah Ya zaɓa mana:

Ni Musulmi ne, kuma wannan shi ne sunan da Ubangijina Ya ba ni.

Akwai hujjoji daga Sunnah da ke nuna cewa sunan da Allah Ya zaɓa wa mabiyan wannan addini shi ne "Musulmai", ba "Muhammadawa" ba.

Annabi Muhammad (SAW) bai taɓa koyar da sahabbai su kira kansu "Muhammadawa" ba. A maimakon haka, duk lokacin da aka ambaci mabiyan addinin, ana cewa:
Musulmai
Muminai
Ahlul-Islam

Sahabbai ma ba su taɓa kiran kansu Muhammadawa ba.

Dalilin da ya sa malamai da yawa s**a ƙi wannan suna shi ne saboda yana iya ba da tunanin cewa addinin ya danganci mutum ne (Muhammad SAW), alhali Musulunci addini ne na bautar Allah Shi kaɗai.

Annabi (SAW) ya kasance Manzon Allah ne, ba abin bauta ba.

Sunan da ya dace da koyarwar Alƙur'ani da Sunnah, kuma wanda musulmai s**a yarda da shi tun zamanin sahabbai, shi ne "Musulmi".
Allah Ya zaɓi sunan Musulmai.

Annabi (SAW) da sahabbai sun yi amfani da wannan suna.

Ba a samu sunan "Muhammadawa" a matsayin sunan da Annabi ya sanya wa al'ummarsa ba.

Don haka mafi dacewa kuma mafi bin Sunnah shi ne mutum ya ce:
"Mu Musulmai ne", ba "Mu Muhammadawa ne ba.

Allah Ya haɗa zukatan musulmai a kan gaskiya, Ya nisantar da mu daga son rai da rarrabuwar kawuna. Ameen.

-Ibrahim Muhammad Dantata.

Ganin Allah, Annabawa da Bayin Allah Salihai Ta Fuskar Ruhaniya.Idan ana magana a kan ganin Allah, Annabawa ko bayin All...
05/06/2026

Ganin Allah, Annabawa da Bayin Allah Salihai Ta Fuskar Ruhaniya.

Idan ana magana a kan ganin Allah, Annabawa ko bayin Allah salihai, wajibi ne a bambanta tsakanin abin da yake tabbatacce da hujjojin Alƙur’ani da Sunnah, da kuma abin da malamai s**a ambata a matsayin kwarewar ruhaniya (kashfi, mushahada ko ru'ya).

1. Ganin Allah a Wannan Duniya:

Aƙidar Ahlus-Sunnah wal-Jama’ah ita ce babu wani mutum da zai ga Allah Maɗaukakin Sarki da idon zahiri a wannan duniya.

Allah Ya ce wa Annabi Musa (AS):

وَلَمَّا جَاءَ مُوسَىٰ لِمِيقَاتِنَا وَكَلَّمَهُ رَبُّهُ قَالَ رَبِّ أَرِنِي أَنْظُرْ إِلَيْكَ ۚ قَالَ لَنْ تَرَانِي وَلَٰكِنِ انْظُرْ إِلَى الْجَبَلِ فَإِنِ اسْتَقَرَّ مَكَانَهُ فَسَوْفَ تَرَانِي ۚ فَلَمَّا تَجَلَّىٰ رَبُّهُ لِلْجَبَلِ جَعَلَهُ دَكًّا وَخَرَّ مُوسَىٰ صَعِقًا ۚ فَلَمَّا أَفَاقَ قَالَ سُبْحَانَكَ تُبْتُ إِلَيْكَ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُؤْمِنِينَ
(الأعراف: 143)

"Lokacin da Musa ya zo wurin alƙawarinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, sai ya ce: 'Ya Ubangijina! Ka nuna mini Kanka in kalle Ka.' Sai Allah Ya ce: 'Ba za ka gan Ni ba (لَنْ تَرَانِي), amma ka dubi dutsen nan; idan ya tsaya a wurinsa, to za ka gan Ni.' Da Ubangijinsa Ya bayyana wa dutsen, sai Ya mai da shi niƙaƙƙe, Musa kuma ya faɗi a sume. Da ya farfaɗo sai ya ce: 'Tsarki ya tabbata gare Ka! Na tuba zuwa gare Ka, kuma ni ne na farko daga cikin muminai.'"

A wajen malamai na Ahlus-Sunnah, kalmar "لَنْ تَرَانِي" a wannan aya ita ce hujjar cewa Annabi Musa (AS) bai ga Allah da idon zahiri a duniya ba.

Amma ayar ba ta kore yiwuwar ganin Allah a Lahira ba, domin akwai wasu ayoyi da hadisai sahihai da s**a tabbatar da ganin Allah ga muminai a Aljanna.

Haka kuma, lokacin da aka tambayi Annabi ﷺ ko ya ga Ubangijinsa, sai ya ce:
سَأَلْتُ رَسُولَ اللَّهِ ﷺ: هَلْ رَأَيْتَ رَبَّكَ؟ فَقَالَ: نُورٌ أَنَّى أَرَاهُ

"Na tambayi Manzon Allah ﷺ: Shin ka ga Ubangijinka? Sai ya ce: 'Haske ne, ta yaya zan gan Shi?'"
(Sahih Muslim)
A wata ruwayar kuma:
رَأَيْتُ نُورًا

"Na ga haske."

Wadannan hadisai suna daga cikin hujjojin da malaman Ahlus-Sunnah s**a kawo cewa Annabi ﷺ bai ga Allah da idon zahiri na duniya ba, domin shi da kansa ya bayyana cewa akwai hijabin haske tsakaninsa da ganin Ubangijinsa a wannan yanayi.
Sai dai malamai sun yi sabani kan ko ya gan Shi da zuciya a daren Mi'iraji, amma mafi yawan malaman hadisi sun tafi a kan cewa bai gan Shi da idon zahiri ba.

Saboda haka, ganin Allah da idon zahiri a wannan rayuwa ba abu ne da nassoshi s**a tabbatar ba.

2. Ganin Allah a Lahira:

Ganin Allah a Lahira Ahlus-Sunnah sun yi ittifaki cewa muminai za su ga Ubangijinsu a Lahira, kuma wannan yana daga cikin mafi girman ni'imomin Aljanna.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

﴿وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَاضِرَةٌ . إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ﴾
— سورة القيامة:
"Wasu fuskoki a ranar nan za su kasance masu annuri, suna kallon Ubangijinsu." (Suratul Qiyamah: 22–23)

Haka kuma hadisan Annabi ﷺ masu yawa sun tabbatar da wannan ni'ima mai girma.

3. Ganin Annabi ﷺ a Mafarki:

Ganin Annabi ﷺ a Mafarki Wannan kuwa tabbataccen al'amari ne da ya zo a cikin hadisan sahihai.
Annabi ﷺ ya ce:

﴿مَنْ رَآنِي فِي الْمَنَامِ فَقَدْ رَآنِي، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ لَا يَتَمَثَّلُ بِي﴾
— رواه البخاري ومسلم.
"Duk wanda ya gan ni a mafarki, to hakika ya gan ni, domin Shaiɗan ba zai iya k**anni na ba." (Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim)

Saboda haka, ganin Annabi ﷺ a mafarki gaskiya ne idan ya zo cikin siffofinsa na gaskiya.

4. Ganin Annabawa da Salihan Bayi Ta Ruhaniya

وقد رُوي عن كثير من العلماء والأولياء أن الله تعالى قد يفتح لبعض عباده أبواب الكشف والمشاهدة، حتى يروا بعض الأنبياء أو الصالحين في المنام أو في أحوالٍ روحانية.
وقد ذكر عددٌ من العلماء إمكانَ هذه الكرامة، إلا أنهم بيّنوا أن:
ذلك من المواهب والكرامات التي يختص الله بها من يشاء من عباده.
لا يُبنى عليه حكمٌ شرعي، ولا يُعارض نصوص الكتاب والسنة.
يُقبل إذا وافق الشرع، ويُردّ إذا خالفه.
وليس شرطًا في الإيمان ولا دليلًا على الأفضلية المطلقة.

An ruwaito daga malamai da waliyyai da dama cewa Allah kan buɗe wa wasu bayinsa ƙofofin kashfi da mushahada, har su ga wasu daga cikin Annabawa ko salihan bayi a mafarki ko a wani yanayi na ruhaniya.

Malamai da dama sun ambaci yiwuwar irin wannan baiwa, amma sun yi bayanin cewa:

هذا لا يبلغ مرتبةَ الحُجَّة الشرعية.
ولا تُبنى عليه الأحكامُ الشرعية.
ويجب أن لا يُخالف القرآنَ الكريم والسنةَ النبوية.
ومن حصل له شيءٌ من ذلك، فهو أمرٌ بينه وبين الله تعالى.

Wannan bai kai matsayin hujjar shari'a ba.

Ba a gina hukunce-hukuncen addini a kansa.

Dole ne ya kasance bai saɓa wa Alƙur’ani da Sunnah ba.
Wanda ya samu irin wannan hali, al'amari ne tsakaninsa da Allah.

5. Matsayin Kashfi a Musulunci:

ذكر عددٌ من كبار العلماء، مثل عبد القادر الجيلاني، وأبي حامد الغزالي، وابن تيمية، أن الكشف قد يقع لبعض عباد الله الصالحين.
Manyan malamai k**ar su Abdul Qadir al-Jilani, Abu Hamid al-Ghazali da Ibn Taymiyyah sun ambaci cewa kashfi na iya faruwa ga wasu bayin Allah na gari.

Sai dai dukansu sun jaddada cewa:
Alƙur'ani da Sunnah su ne ma'aunin gaskiya, ba kashfi ba.

Duk wani kashfi ko mushahada da ya saɓa wa Alƙur'ani da Sunnah ba za a karɓe shi ba.

Ganin Allah da idon zahiri a wannan duniya ba shi da hujja tabbatacciya a Shari'a.

Ganin Allah a Lahira tabbatacce ne da Alƙur’ani da Sunnah.

Ganin Annabi ﷺ a mafarki tabbataccen al'amari ne.

Ganin Annabawa ko salihan bayi ta hanyar mafarki, kashfi ko mushahada wani abu ne da malamai s**a ambata a matsayin baiwar Allah ga wasu bayinsa, amma ba hujjar da za a tilasta wa kowa yarda da ita ba.

Saboda haka, ana iya cewa Allah Maɗaukakin Sarki yana keɓance wasu bayinsa da baiwar abubuwan ruhaniya da ba kowa ne yake samu ba.
Wanda bai samu irin wannan hali ba, ba lallai ne ya fahimci hakikarsa ba.

Haka kuma, imanin mutum da irin waɗannan abubuwa ko rashin imaninsa ba shi ne ma'aunin samuwarsu ko rashin samuwarsu ba, domin al'amari ne da ya danganci abin da Allah Ya keɓanta wasu daga cikin bayinsa da shi.

Alhamdulillāhi Rabbil ‘ālamīn. Ina miƙa godiya ta musamman ga Allah Madaukaki da Ya azurta ni da fahimta da nutsuwar ruhaniya. Ina roƙonSa da Ya ƙara mana ilimi mai amfani, Ya tabbatar da zuciyarmu a kan gaskiya, Ya tsarkake mu daga kuskure da shakku, Ya kuma sanya wannan fahimta ta zama haske da dalilin ƙarin kusanci gare Shi da kyautatuwar ibadata. Allah Ya karɓi wannan daga gare ni, Ya kuma tabbatar da mu duka a kan hanya madaidaiciya.

— Ibrahim Muhammad Dantata.

Riya, son girma, neman dukiya, da rikicin neman gadon malunta sun bayyana a cikin wasu kungiyoyin addini na Musulunci. W...
18/05/2026

Riya, son girma, neman dukiya, da rikicin neman gadon malunta sun bayyana a cikin wasu kungiyoyin addini na Musulunci.

Wasu masu da’awar malunta sun mayar da addini hanyar neman duniya, neman suna yawan jayayya, rikici, da fafatawa saboda kuɗi, suna, da iko. Wannan lamari ya yi k**a da abin da ya faru a tsofaffin addinai a tarihi. Abin takaici, a wasu lokuta ana ganin wasu malamai ba sa nuna tsoron Allah ko jin kunyar mabiyansu wajen irin waɗannan halaye.

A wasu lokuta na wannan zamani ana yawan samun masu riya, da son mulki, da neman dukiya, da rikice-rikice tsakanin masu da’awar jagoranci na addini — ba a kawai cikin kiristoci da yahudawa ba kaɗai, har ma a addinin Musulunci a wannan zamani.

Allah a cikin Al-Qur’ani ma ya yi gargadi game da malamai ko shugabanni da suke amfani da addini domin neman abin duniya:

Allah ya na cewa:

وَءَامِنُواْ بِمَآ أَنزَلۡتُ مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَكُمۡ وَلَا تَكُونُوٓاْ أَوَّلَ كَافِرِۢ بِهِۦۖ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِ‍َٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗا وَإِيَّٰيَ فَٱتَّقُونِ.

“...Kada ku sayar da ayoyina da ɗan ƙaramin farashi....”
— Suratul Baqarah 2:41

Haka kuma akwai hadisan da suke gargadin neman shugabanci ko yin addini domin neman yabo da anfani na duniya.

Wannan yana nuna cewa matsalar ba sabuwa ba ce, Sai dai tayi k**ari a wannan zamani fiye da zamanai na baya.

Duk da haka yana da muhimmanci a bambanta tsakanin:
kuskuren wasu mutane masu amfani da addini, da addinin kansa ko dukkan malamai baki ɗaya.

A cikin tarihi akwai malamai na Musulunci masu gaskiya da tsoron Allah da s**a sadaukar da rayuwarsu wajen ilimi, adalci, da taimakon jama’a, k**ar Imam Abu Hanifa, Imam Malik, Imam al-Nawawi, da sauransu.

Haka kuma akwai waɗanda s**a shiga rikice-rikicen siyasa, da neman dukiya, ko neman mabiya.

Allah a cikin Qur’ani Mai girma ya gargadi muminai kada su bi mutane makaho-makaho:

وَمَا يَتَّبِعُ أَكۡثَرُهُمۡ إِلَّا ظَنًّاۚ إِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡ‍ًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا يَفۡعَلُونَ.

“Kuma mafi yawansu ba sa bin komai face zato....”
— Suratu Yunus 10:36

Rikice-rikicen neman jagoranci da ake gani a wasu dariku da kungiyoyin addini, k**ar rikicin shugabanci tsakanin wasu manyan malamai a Kadiriyya, da Tijjaniyya, da kuma rikice-rikicen cikin Izala, sun sa mutane da yawa suna ganin cewa akwai son mulki, neman suna, tara magoya baya, da anfani na duniya a cikin wasu daga cikin wadannan sabani.

Yawaitar cece-kuce, rabuwar kai, da fafatawa tsakanin masu da’awar jagoranci na addini na kara jefa mutane cikin shakku kan sahihancin niyya da manufar wasu daga cikin masu wannan ikirari.

Saboda haka, ya dace mutum:
ya yi amfani da hankali da bincike,
ya auna maganganu da hujja,
ya guji ɗaukaka mutum, ya bar gaskiya,
kuma ya rika kallon ɗabi’a da ayyuka ba kawai magana ko sutura ba.

Kuma a guji yanke hukunci cewa “duk malamai” haka suke, domin hakan ma rashin adalci ne. A ko da yaushe akwai nagari da marasa nagarta a cikin kowace al’umma ko kungiya.

-Ibrahim Muhammad Dantata

14/05/2026

Akwai wata mummunar manufa ta siyasar Duniyar yahudawa da kiriaroci da ta sojojin ta daga ƙasashen Yamma, musamman United States da Israel, wace suke bi domin ƙarfafa tasirinsu a Duniya da kuma yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kokarin rage ƙarfin ƙasashen musulmai a Duniya.
Musamman bayan hashashen da s**a yi na kawar da Jamhuriyar musulunci ta kasar Iran.
Wannan shi ne batun abin da suke kira “Greater Israel,” wato faɗaɗa ikon Isra’ila a yankin.

Sai dai duk da irin ƙarfin iko, mak**ai, da tasirin siyasa da waɗannan ƙasashe suke da shi, tarihi ya nuna cewa babu wani iko da zai rinjayi ikon Allah Maɗaukakin Sarki.

Duk wanda ya ɗauki kansa a matsayin wanda babu mai iya kalubalantarsa, lokaci kan bayyana rauninsa da gazawarsa.

Allah Shi kaɗai ne Mabuwayi, Mai rinjaye bisa komai, wanda yake ɗaukaka wanda Ya so kuma Ya ƙasƙantar da wanda Ya so.

Abin mamaki shi ne, abubuwan da suke tsammanin za su ƙarfafa su ne suke yawan zama sanadin fallasar rauninsu a idon duniya.

Tun daga lokacin da s**a fara hare-hare da zalunci a kan marasa ƙarfi, duniya ta fara ganin yadda rikice-rikice, rarrabuwar kawuna, da matsin lamba suke ƙaruwa a cikinsu. Wannan yana ƙara tunatar da mutane cewa zalunci ba ya dawwama, kuma ƙarshen masu girman kai yana zuwa ne a hankali, ko da kuwa sun ɗauki kansu a matsayin manyan masu iko.

Musulmai suna da imani cewa duk wata makirci ko ƙulla sharri ba zai yi nasara ba face abin da Allah Ya ƙaddara. Saboda haka abin da ya fi dacewa ga al’umma shi ne haɗin kai, ilimi, adalci, haƙuri, da dogaro ga Allah, domin Shi ne Gagara Misali, Mai ikon canja al’amura cikin kiftawar ido.

Muna gode wa Allah Maɗaukakin Sarki, Wanda Ya nuna mana cewa iko da nasara suna hannunsa Shi kaɗai. Hakika abin farin ciki ne ganin yadda ɗaya daga cikin ƙasashen musulmi ta samu ƙarfin guiwa da damar tsayawa domin kare martaba da muradun al’ummar Musulmi, a lokacin da wasu manyan azaluman ƙasashe masu iko suke ƙoƙarin kakaba zalunci da tsoratarwa a kan musulmai na duniya.

Wannan ya zama wani babban tunatarwa cewa al’ummar Musulmai ba marasa ƙarfi ba ne idan s**a haɗu, s**a dogara ga Allah, s**a kuma tsaya kan gaskiya da adalci.

Duk wani ƙoƙari na jefa musulmai cikin tsoro, wulakanci, ko rushe martabarsu ba zai dawwama ba, domin Allah Shi ne Mafi Girma kuma Mafi Ƙarfi a kan kowane irin iko na duniya.
Abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne musulmai su ƙara haɗin kai, su nisanci rarrabuwar kawuna, su rungumi ilimi, hikima, da haƙuri, tare da dogaro ga Allah a cikin dukkan al’amuransu.

Domin tarihin duniya ya nuna cewa duk wata daula da ta gina ikonta a kan zalunci da girman kai, daga ƙarshe tana fuskantar raunana da rushewa.

-Ibrahim Muhammad Dantata.

TAKAITACCIYAR  GABATARWA DA KARIN BAYANI KAN KANO CHRONICLE(Wanda H. R. Palmer ya fassara tare da gabatarwa)Mece ce Kano...
29/07/2025

TAKAITACCIYAR GABATARWA DA KARIN BAYANI KAN KANO CHRONICLE

(Wanda H. R. Palmer ya fassara tare da gabatarwa)

Mece ce Kano Chronicle?

Kano Chronicle wani tsohon littafi ne da ke ƙunshe da tarihin sarakunan Kano tun daga farkon kafuwar Kano har zuwa lokacin da Fulani s**a karɓi mulki a shekara ta 1807. Wannan littafi ya ƙayade sunayen sarakuna da zamanin mulkinsu, ayyukansu, gina gari da gine-gine, yaƙe-yaƙe, da kuma yadda Musulunci ya shiga Kano.

Waye ya fassara wannan Tarihi?

Wani baturen mulkin mallaka mai suna H. R. Palmer ne ya fassara Kano Chronicle daga rubutun Larabci zuwa Turanci. Ya kuma rubuta wata gabatarwa mai tsawo da ke ƙunshe da cikakken bayani kan tarihin Kano da Hausawa gaba ɗaya.

Asalin Kano Chronicle

Palmer ya ce an samo kwafin wannan Chronicle daga Sabon Gari kusa da Katsina. Ko da yake takardar ba tsohuwa sosai ba ce, amma ana ganin tana wakiltar wani tsohon tarihi da ya ɓace. An fi tunanin an rubuta wannan Chronicle ne a tsakanin shekara ta 1883 zuwa 1893, amma labaran da ke cikinta sun faru ne tun daga ƙarni na 10 zuwa ƙarni na 19 Miladiyya.

Menene littafin ya ƙunsa?

1. Jerin Sarakunan Kano daga Bagauda har zuwa Muhammadu Bello.

2. Tarihin shigowar Musulunci zuwa Kano da Hausaland gaba ɗaya.

3. Zuwan Wangarawa daga Mali da tasirin da s**a yi a wajen ɗaukaka Musulunci.

4. Bayani kan Bayajidda da asalin daulolin Hausa bakwai (Daura, Kano, Katsina, Zazzau, Gobir, Rano da Biram).

5. Siffofi da al’adun Hausawa kafin zuwan Fulani.

6. Mamayewar Fulani da kafa mulkin jihadi a 1804–1807.

Asalin Hausawa da mamayewar Fulani

Palmer ya kawo ra’ayoyi daban-daban kan asalinsu Hausawa, inda ya nuna cewa akwai yiwuwar sun samo asali daga wata kabila da ake kira “Sa” ko “Sau” – waɗanda ake danganta su da maciji a tatsuniyoyi. Wannan ya yi daidai da labarin Bayajidda da matsan shudi a Daura. Hakanan, an danganta Hausawa da wasu kabilun Mali k**ar Wangarawa, da kuma kabilun Libya (Hamitic) da Larabawa (Semitic) da s**a zo daga gabas da arewa.

Fulani kuwa, sun mamaye Kano da sauran ƙasashen Hausa ne a ƙarshen ƙarni na 18 da farkon na 19, lokacin da Shehu Usman Ɗan Fodio ya fara Jihadi da nufin gyaran addini da kawar da sarakunan da ya kira “kafurai”.

Waye ya rubuta Chronicle?

Ba a san marubucin Kano Chronicle ba. Amma daga salon rubutun da kalmomin da aka yi amfani da su, Palmer ya ce yana da yiwuwar marubucin ba mallamin Fulani ba ne, kuma ya fi k**a da wani bawan Allah daga Kano ko kusa da Kano wanda ya tattara tarihi ta baki da labaru daga mutane.

Me yasa wannan Tarihi ya fi muhimmanci?

1. Tarihi daga mahangar Hausawa: Chronicle ɗin yana ɗauke da tarihin sarakuna k**ar yadda Hausawa da kansu s**a sani kafin mamayewar Fulani.

2. Ba da cikakken jerin sarakuna: Ya kawo sunaye da bayanai kan sarakunan Kano 48 tun daga Bagauda har zuwa Muhammadu Bello.

3. Shaidar shigowar Musulunci: Ya tabbatar da cewa Musulunci ya fara shigowa tun kafin Fulani, musamman a zamanin Sarki Yaji da Sarki Rumfa.

4. Tarihi mai cin gashin kansa: Chronicle ya ƙunshi bayanai masu zurfi da basu nuna goyon baya ga Fulani ko kabilanci ba, shi ya sa Palmer ya yarda da sahihancinsa.

Menene alaƙar Kano da wasu dauloli?

Kano ta sha hulɗa da daulolin Ghana, Mali, Bornu, da Masar.

An ambaci malamai k**ar Abdul Magili wanda ya ziyarci Kano daga Tuat (Aljeriya) kuma ya rubuta wasiƙa zuwa Sarki Muhammad Rumfa.

An ce Wangarawa daga Mali sun taimaka wajen yada Musulunci a Kano.

Fulani kuwa sun karɓi mulki ne daga Habe, wato sarakunan gargajiya da s**a gaji mulki tun zamanin Bayajidda.

Matsayi da kima:

H. R. Palmer ya nuna cewa Kano Chronicle yana da matuƙar kima a ilimin tarihi, musamman ga masu nazari kan:

Tarihin Hausawa,

Tasirin Musulunci,

Mulkin gargajiya a Arewacin Najeriya,

Da ƙaddamar da jihadi da mamayewa da sauyin siyasa.

Kano Chronicle littafi ne da ke bayyana tarihin Kano da Hausawa kafin da bayan zuwan Fulani. Fassarar H. R. Palmer ta taimaka wajen bayyana muhimman abubuwa k**ar asalin sarakuna, shigowar Musulunci, al’adun gargajiya, da yanayin siyasa. Duk da cewa akwai wasu ɓangarori da suke buƙatar ƙarin bincike, Chronicle din yana ɗaya daga cikin tushe mafi muhimmanci a tarihin Arewacin Najeriya.

TARIHIN KANO

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai.
Salati da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu (SAW), fiyayyen halitta.

Wannan shi ne tarihin sarakunan da s**a shugabanci ƙasar Kano, tun daga tushe har zuwa zuwan Musulunci. Tarihin yana farawa ne da wani mutum mai suna Barbushe, wanda ya fito daga zuriyar wani sanannen mutum mai suna Dala.

Asalin Barbushe da Dala

Barbushe mutum ne bakar fata, dogo, mai ƙarfi, kuma ƙwararren mafarauci. Dala, kakansa, ya zo Kano daga wani wuri da ba a sani ba, ya zauna a kan tsaunin da ake kira Dutsen Dala. A nan ya gina gida tare da matansa, inda s**a haifi yara bakwai: maza huɗu da mata uku. Babban ɗansu shi ne Garageje, wanda daga gare shi ne aka haifi Buzame, mahaifin Barbushe.

Barbushe ya gaji ilimin al’adun kakanninsa ko Kuma ya koyi bokanci da tsafi daga baya Kuma ya ci gaba da rayuwa bisa addinin bautar aljanu. Ya zama shugaba a cikinsu ta hanyar sihiri da wasu ƙwararrun ilimai na al’adu, kuma ya mallaki iko fiye da sauran shugabanni.

Jagoranci da Shaharar Barbushe

Daga cikin manyan mutanen da ke ƙarƙashin Barbushe akwai:

Guizago – wanda ke zaune a ƙasan Dutse Gorondutse a gabas.

Gagiwa – mahaifin Rubu, mutum mai ƙarfi sosai, har yana k**a giwaye da igiya.

Gubanasu, Ibrahim, Bardoje, Nisau, Kanfatau, Doje, Janbere, Gaiuakira, Safataro, Hangogo da Gartsangi – waɗannan duka manyan mutane ne masu daraja da matsayi a ƙasar.

Tsamburo ya zauna a Jigiriya, Jandarmisa a Magum. Shi ne ake danganta zuriyar Rumawa da shi. Daga Gogau zuwa Salamta, mutane na kiran kansu Rumawa saboda sun samu girma da iko.

Hambaro ya zauna a Tanagar, Gambarjado (ɗan Nisau) ya zauna a Fanisau.

Wadannan duka – waɗanda s**a rayu kafin Musulunci ya iso – ba su kasance Musulmai ba. Su ne s**a rike al’adun ƙabilanci na bautar gumaka da al’adun gargajiya.

Addinin Gargajiya da Bautar Gumaka

Mutane daga ƙauyuka daban-daban, daga Doji zuwa Dankwoi, da Toda zuwa Dan Bakohshi, s**an taru wajen Barbushe a ranakun biyu na Sallar Hadaya (Idi), domin gudanar da hadaya da bauta.

Wurin bauta mafi daraja shine Kakiua (ko Kagua), kuma gumakan da ake bauta musu sunansa Tchunburburai – wata itace ce mai suna Shamuti.
Mutum na musamman ne kawai yake iya zama kusa da wannan itace – ana kiransa Mai-Tchunburburai. An zagaye itacen da katanga mai tsarki – babu wanda zai shiga ciki sai Barbushe kadai. Duk wanda ya shiga, in ba shi ba, zai mutu.

Barbushe yana sauka daga Dutsen Dala ne kawai a ranakun biyu na Idi.
A irin waɗannan ranaku, maza da mata daga gabas da yamma, kudu da arewa, s**an zo da hadaya:

Kare baki

Kaza baka

Akuya baka

Duk waɗannan domin sadaukarwa ne ga gumakan su.

Da dare na Juma’a ya sauka, Barbushe zai fito daga gidan tsauni tare da masu kaɗa ganga. Sai ya ɗaga murya ya ce:

"Uba mai girma na Jimuna, mun zo kusa da mazauninka don roƙo, Ta chunburburai."

Mutane kuma su amsa da cewa:

"Ku kalli Ta chunburburai, ku mutanen Kano! Ku kalli Dala!"

Bayan haka sai Barbushe ya tafi da su zuwa wajen gumakan. Idan s**a isa, s**an yanka hadayarsu – ko kare, ko akuya – a matsayin sadaukarwa.

Iko da Mu’ujiza

Barbushe yana shiga cikin wurin tsarkakakke shi kaɗai, ya ce:

"Ni ne magajin Dala. Ko kun so, ko ba ku so, dole ne ku bi ni."

Mutane kuma su ce:

"Kai ne mai dutsen Dala, ubangijin Mamale, dole ne mu bi ka."

Sai su yi ta zagaye a kusa da gumaka har gari ya waye, su fita tsirara, su ci abinci a cikin wannan rana ta bauta.

Bayan haka, Barbushe zai faɗi abin da zai faru cikin shekara mai zuwa – ko baƙin hari, ko yunwa, ko albarka.

Ya taba faɗin hasashen cewa:

"Mulkinku zai ƙare. Wannan itace (Tachunburburai) za a sare ta. Za a gina masallaci a wannan wuri. Wani mutum zai zo daga nesa, tare da rundunarsa, ya mulke ku har abada."

Mutanen sun tsorata, s**a tambaye shi:

"Wai me ya sa ka faɗi haka? Wannan magana mai muni ce!"

Amma ya amsa da cewa:

"Idan ba a zamaninku ba ne, to a zamanin ’ya’yanku ne. Za ku shaida hakan."

📜 TARIHIN BAGAUDA

Zuwan (Bagauda).
Daga baya, bayan rasuwar Barbushe da wasu shekaru, sai ga wani mutum da ake kira Bagauda ya zo da rundunarsa. Wasu na ce wa Bagauda ne ya fara zuwa Kano; wasu kuma cewa ɗan dansa ne ko jikansa.

A lokacin da ya iso, ya tarar da manyan daga cikin mutanen Barbushe:

Janbere

Hambaro

Gartsangi

Jandarmisa

Kanfatau

S**a tambaya juna:

"Shin wannan shi ne mutumin da Barbushe ya faɗa mana game da shi?"

Janbere ya ce:
"Ina rantsuwa da Tchunburburai, idan kuka bar su su zauna, za su mallake ku har abada."

Amma mutane s**a raina shi, s**a ce:

"Ina Bagauda zai iya cin mu?"

Bagauda shi ne sarkin farko na masarautar Kano. Ya kasance ɗan Bawo ɗan Abu Yazid ( Bayajida) da wata mace mai suna Karbagari.

Wanene Abu Yazid ?

Abu Yazid Wanda ake kira a ƙasar Hausawa da Bayajida shi ne jarumin da ake ɗauka a matsayin tushe na sarakunan Hausa Bakwai. A cewar tatsuniyar gargajiya:

Bayajida ya fito ne daga ƙasar Baghdad (wata tsohuwar ƙasa a Gabas ta Tsakiya).

Ya bar ƙasarsu bayan ya samu matsala da mahaifinsa sarki, ya yi tafiya mai nisa har ya iso Daura (a yanzu cikin jihar Katsina).

A lokacin da ya isa Daura, mutane na fama da matsala, saboda wani maciji mai suna Sarki yana hana su ruwa daga rijiyar Kusugu.

Bayajida ya kwana a gidan wata mata tsohuwa, daga nan ya fahimci halin da suke ciki.

Da sassafe ya je rijiya, ya kashe macijin da takobinsa.

A sak**akon wannan jarumta, Sarauniya Daurama ta ba shi kyauta kuma ta aureshi.

Daga auren nan aka haifi Bawo, wanda ya ci gaba da kafa zuri’ar sarakunan Hausawa.

A cewar Kano Chronicle, Bagauda ya zo Kano ne tare da mutanensa daga yankin Daura ko kusa da Katsina.

Lokacin da ya iso Kano, yankin yana cike da dazuka. Amma ya sami nasarar ƙarfafa mulki da kafa sabon tsari.

Ya kafa birnin Kano kuma ya gina tsohon gidan sarki.

Bagauda ya kafa gidan sarauta na Kano, kuma ya fara jerin sarakunan Kano da s**a biyo bayansa.

Ya yi mulki na dogon lokaci, amma bisa Magana Mafi iganci, ba daga zuri’arsa ne aka haifi shahararrun sarakuna k**ar Sarkin Kano Sultan Muhammadu Rumfa da Sarkin Kano Sultan Muhammad Alwali ba.

"Hakika, Tarihi ba wani abu bane da ya tsaya cak – yana iya sauyawa ko sabuntawa idan an samu sabbin hujjoji ko karin bayani da s**a fi na baya inganci ko sahihanci.

Ga wasu dalilan da yasa tarihin ke sauyawa:

1. Sabbin Gano-gano (Archaeological Discoveries)
Idan masu bincike sun tono wata sabuwar takarda, kayan tarihi, ko rubuce-rubuce da ke ba da wata sabuwar fahimta, hakan na iya sauya yadda ake kallon wani abu da ya faru a baya.

2. Sabon Fahimta ko Fassarori
Masana za su iya duba hujjojin da aka sani tuni, amma su fassara su cikin wani sabon salo ko daga wata sabuwar fahimta. Wannan yana iya sa a sake duban wani bangare na tarihi.

3. Watsuwar Labaran da Aka Boye
Wasu abubuwan da s**a faru a tarihi ana iya ɓoye su saboda siyasa ko son zuciya. Idan daga baya aka bayyana su, s**an sauya fahimtar jama'a game da lokacin da ya gabata.

4. Goge Ƙarya ko Rashin Gaskiya
Wani lokaci wasu bangarori na tarihi an rubuta su ne da son zuciya ko yaudara. Idan aka samu hujjojin da ke kawar da waɗannan ƙagaggun bayanai, tarihi zai gyaru.

Misali:

Tarihin Usman ɗan Fodio da jihad din Shehu an ɗauke shi da girma a baya, amma a zamanin yau ana samun sabbin nazari daga bangaren addini, siyasa da zamantakewa.

Tarihin Kano da ke cikin Kano Chronicle an rubuta shi ne da harshen Ajami, sannan aka fassara shi zuwa Turanci. Amma sabbin nazarin harshe da tarihi na iya fitar da wasu sabbin bambance-bambance da s**a buƙaci gyara fassarar ko ma cikakken sake fasalta tarihin".

-Ibrahim Muhammad Dantata.
Email [email protected]

07/01/2024

أَعُوذُ بِاللّٰهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

وَمَاۤ اَرۡسَلۡنٰكَ اِلَّا رَحۡمَةً لِّـلۡعٰلَمِيۡنَ (١٠٦)

Translation:
We have sent you forth as nothing but salvation and mercy to people of the whole world.
Q. 21:107.

"This verse can also be translated as: We have sent you only as a blessing for the people of the world. In both cases it will mean that the appointment of the Prophet (peace be upon him) is indeed a blessing and mercy of Allah to the whole world. This is because he aroused the neglectful world from its heedlessness and gave it the knowledge of the criterion between truth and falsehood, and warned it very clearly of both the ways of salvation and ruin.
All the smartphones the modernity are as the results of the advents of the holy prophet Muhammad pbuh. Before him world remain in back wards for thousands if not millions of years. Thanks to the advent of Islam and the muslims who were the fathers of all the scientific fields.
Holy prophet is in reality a blessing and salvation of Allah for you.

04/01/2024

أَعُوذُ بِاللّٰهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ.

وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَٰكِن يُضِلُّ مَن يَشَاءُ وَيَهْدِي مَن يَشَاءُ ۚ وَلَتُسْأَلُنَّ عَمَّا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ.

Had Allâh (enforced) His will He would surely have made you (all) one nation (following one and the same faith). But He leaves in error him who wishes (to remain so) and guides him who wishes (to be guided). And you shall surely be called upon to account for your deeds and conduct.
Q.16:93.

"Man has been given freedom of choice. He is free to accept or deny the Reality.
He is responsible for his actions, but is not to be deprived of this freedom, even if he makes mistakes and abuses it.
The uniqueness of the human situation lies in his psychosocial volition. This is the mainspring of human potential - this is what enables him to rise to the highest pinnacle or to fall into the deepest abyss.

The dangers of misuse of freedom continue to confront man throughout his career on the earth. The challenge from Satan is unceasing.
To safeguard man against this, Divine Guidance is to be provided. The trial of Adam and Eve reveals, on the one hand, the essential goodness of their nature and on the other, their susceptibility to error. This demonstrates man's need for Divine Guidance.

Man has not been totally protected against error. This would involve negation of the freedom of choice. He may commit errors; his redemption lies in his realization of that error, in seeking repentance and in turning back to the right path.

The theory of vicegerency affirms that God's creation is deliberate amid not fortuitous. Man has been created with a purpose. Everything else in the creation has been harnessed to his service.

His career on the earth begins with the consciousness of a mission, not through gropings in darkness. The ideal was set before him through Divine revelation.

The criterion for success has been laid down in clear terms. The signposts of the Right Path have been made manifest.

Man's life on earth is in the nature of a trial. It is time-bound.
This Life will be followed by an eternal life wherein man shall reap rewards of his performance in this life.

And in this lifelong trial, men and women are equal participants and will be judged as such. No one is a mere shadow of the other, but both are active co-partners.

The holy Qur'an explicitly states that man and woman will get what they strive for and that the same standard is set for them both as the ultimate criterion for their success.

وَالۡمُؤۡمِنُوۡنَ وَالۡمُؤۡمِنٰتُ بَعۡضُهُمۡ اَوۡلِيَآءُ بَعۡضٍ‌ۘ يَاۡمُرُوۡنَ بِالۡمَعۡرُوۡفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ الۡمُنۡكَرِ وَيُقِيۡمُوۡنَ الصَّلٰوةَ وَيُؤۡتُوۡنَ الزَّكٰوةَ وَيُطِيۡعُوۡنَ اللّٰهَ وَرَسُوۡلَهٗ‌ؕ اُولٰۤئِكَ سَيَرۡحَمُهُمُ اللّٰهُؕ اِنَّ اللّٰهَ عَزِيۡزٌ حَكِيۡمٌ ٧١ وَعَدَ اللّٰهُ الۡمُؤۡمِنِيۡنَ وَالۡمُؤۡمِنٰتِ جَنّٰتٍ تَجۡرِىۡ مِنۡ تَحۡتِهَا الۡاَنۡهٰرُ خٰلِدِيۡنَ فِيۡهَا وَمَسٰكِنَ طَيِّبَةً فِىۡ جَنّٰتِ عَدۡنٍ‌ ؕ وَرِضۡوَانٌ مِّنَ اللّٰهِ اَكۡبَرُ‌ ؕ ذٰ لِكَ هُوَ الۡفَوۡزُ الۡعَظِيۡمُ  ٧٢

"And the believers, the men and the women, are friends protecting each other; they seek and enjoin good and forbid evil and offer the prayer and pay the Zakat (poor-due): and they obey God and His Messenger. It is on these whom Allah will have mercy. Surely Allah is All-Mighty, All-Wise. Allah has promised to the believers, men and women, gardens underneath which rivers flow, forever therein to dwell, and goodly dwelling-places in the gardens of Eden, and greater than anything else, God's good pleasure (and acceptance from Him). That is the supreme triumph."
9:71-72.

It also says:

وَمَنۡ يَّعۡمَلۡ مِنَ الصّٰلِحٰتِ مِنۡ ذَكَرٍ اَوۡ اُنۡثٰى وَهُوَ مُؤۡمِنٌ فَاُولٰٓئِكَ يَدۡخُلُوۡنَ الۡجَـنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُوۡنَ نَقِيۡرًا. ٤:١٢٤

And whosoever does a righteous deed, be they male or female, and is a believer, we shall assuredly give them a goodly life to live; and We shall certainly reward them according to the best of what they did."
Q.,4:124.

Address

101 Kurna-madatai Quarters
Kano

Telephone

+2348037781792

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zauren_Makaranta posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zauren_Makaranta:

Share

Category