08/09/2022
*ƘISSAR DATA SANI CANZA HALAYE NA*💔😭
Mansur Bn Ammar Yace "Ina da Wani Aboki Mai Yawan Saɓon Allah, Sai ya Tuba ya zama mai yawan Ibadu da sallar dare, Wata rana Sai aka kwan biyu ban ganshi ba, dana tambaya aka cemun" Ai Bashi da lafiya ne" sai na Je Gidan sa,da ya'rsa ta fito Sai na aikata cewar "tacewa babanta wane ne" bayan na shiga sai na sameshi a Farfajiyar gidan a kishingiɗe sai naga fuskarsa tayi Baƙi Ƙirin, idonsa Sun Kafe, bakinsa ya bushe, Sai ya ban Tsoro😢 Nace "Ya Ɗan Uwa, yawaita Faɗin LA ILAHA ILLALLAH" sai ya waigo daƙyar ya kalleni nan take sai ya suma, bayan ya farfaɗo sai na sake ce masa "Ya Ɗan Uwa ka yawaita Faɗar LA ILAHA ILLALLAH!" Na sake Faɗa masa sau uku, sai Ya buɗe idonsa yace
*يا أخي منصور! هذه الكلمة قد حيل بيني وبينها*
"Ya Ɗan Uwa Mansur,Wannan kalma (La ilaha illallah) An Katange ni da ita" (ma'ana bazai iya faɗarta ba)
Mansur Bn Ammar Yace "La Haula Wala Quwwata illabillah!!😭 Ya Ɗan Uwa ina Yawan Ibadar Dana sanka dashi?! Kai kuwa Ina yawan Azumin ka?! Ina Tahajjud da Qiyamul-Lailinka? Sai Yace"Ya Ɗan Uwa Mansur! Wlh duk ba domin Allah nayisu ba! Kuma na kasance ina tubar Ƙarya, ina yawan ibada ne kawai dan A Faɗa game Dani, Kuma dan a Riƙa ambato na(Riya), haka nake tsawon lokaci sai yau Allah ya Fallasa ni🥺, Ina Ɓuya a idon mutane in sauke labule, na sha giya nai sauran Saɓo ƙarara gaban ubangiji na😢 - Astagfirullah-
(Abunda ya faru bayan Daɗewata ɗin nan ckn Saɓo)
Watarana Sai Rashin Lafiya ya kamani har nai kusa Mutuwa, sai nasa aka fito dani Farfajiya nacewa ya'ta ta miƙo Alqur'ani, bayan na karanta sai na Roƙi Allah kan ya yaye mun ciwo na Albarkacin wannan Alqur'ani sai Allah ya amsa ya yaye mun, bayan Na Samu sauki sai na koma ckn Saɓon Allah na😭, Tsawon lkc Sai Wani Rashin lafiya ya sameni, Nan ma Na Roƙi a fitar dani Farfajiya na sa aka miƙo mun Alqur'ani na karanta na Sashi a Ƙirjina na Roƙi Allah ya Warkar dani Albarkacin Alqur'ani na masa Alƙawarin Bazan koma saɓa masa ba karo na biyu, Sai Allah ya Amsa mun, bayan na warke Sai na Koma (ckn Saɓo) na Manta Na Shashantar da Alƙawarina ga Ubangiji, Sai na Kamu da wanann ciwo da yanzu kk Gani na ciki😢
(Abunda ya faru a Wannan Karon)
Na Umarci Iyalaina na su Fito dani Farfajiya kmr yadda na saba, nace su miƙo mun Alqur'ani nai karatu, (a wannan karon) Da na Buɗe Alqur'ani Sai Naga Ba ko Harafi Ɗaya a cikinsa, Sai na Fahimci Lallai Ubangijin Al'arshi Yayi Fushi dani! 😭 Sai na Ɗaga kaina sama nace "ubangiji na ka Yaye mun" sai Naji Murya kamar Mai sanarwa, ana cewa
*تتوب عن الذنوب إذا مرضتَ # و *ترجع للذنوب إذا برئتَ؟*
*فـكم من كـربة نجـاك منـها* # *وكم كشف البلاء إذا بليتَ؟*
*أما تخشى بأن تأتي المنايا #*
*وأنت على الخطايا قد تهمتَ؟*
"Kana Tuba A Zunubi in Baka da lafiya daka samu sauki sai ka koma?, Baƙin ciki nawa Allah ya Tserar dakai, kuma sau nawa ana yaye ma bala'in daya sameka? Ashe baka tsoron mutuwa tazo maka kana ckn Saɓo a kewaye?"
Mansur Bn Ammar Yace "Wlh Da Kuka na fita a wajensa, ko Ƙofar Gidan ban isa ba Naji ance ya cika(ya mutu).
*[كتاب"موسوعة الأخلاق والزهد" من ص 14]*
Copied