28/11/2023
MU FADAWA KANMU GASKIYA
A bisa bincike da aka gudanar kwana-kwanan nan daga cikin matasan da suke ta'ammali da kafar yada labarai ta zamani( Social media) a Kano kashi 27% ba su gama Secondary school ba, Kashi 65% masu Secondary ne da NCE da Diploma, Kashi 5% sun kammala first degree, Kashi 3% suna da degree na biyu. Sai jifa-jifan masu PhD a cikinsu. Kashi 90% dinsu duk sun haura shekara 18, Kashi 85% sun yi aure. Wasu na da sana'a wasu babu.(bincike).
Idan ka duba yayan Yan siyasar da wadannan matasa ke fada akansu, kusan Kashi 90% duk suna da degree ko na daya, ko na biyu ko na uku in har mutum ya kai shekara 18 ko sama da haka.
Abin da muke kallo a yau shine irin bautar siyasar da aka saka yayan takalawa, babu pension babu gratuity. Sai tsabar wahala da kudin data.
Nan da wani lokaci kadan iyayen za su dakko yayansu su dora, su kuma gadar da bautar zuwa ga yayansu. Kai Dan talaka ka bautawa uba, kuma za ka bautawa 'da. Kuma babu wata hanyar kaucewa sai ka yi wannan bautar. In har ba ka yi karatu ba sai ka dawwama a wannan bautar ta gado.
Shawara:
1. Ka je ka Nemo admission, ka kaiwa maigidanka, in har bai biyama kudin registration ya kuma dauki nauyin karatunka ba, ta daga ranar ka barshi, ba sonka yake ba.
2. Ka je ka yi Business plan, ka kawo masa, in har bai baka ka yi Business ba to ka rabu da shi Alaji, ba kaunarka yake ba.
3. In ka yi karatu, ya samoma offer ko da kudinsa ne, in bai yi maka haka ba, to wallahi ba kaunarka yake ba.
4. Ya baka mukami komai kankantarsa a Gwamnati (in ka San yana da dama). In baima haka ba, Alaji ka rabu da shi ba kaunarka yake ba.
Babu wani dan siyasa da ya bar dansa ba ya karatu, ko aiki, ko business, to kai me ya sa ba za su baka ba? Soyayya ce ko kiyayya?
Mu tashi mu yiwa kanmu fada, mu nemi na kanmu mu daina yawon maula, ko mu ci mutuncin wani don bambanci siyasa ko kare megidan mu.
Allah Ya Kara karemu, Ya sake hadamu da masu kaunar matasa ameen.