23/05/2026
WACE ALAƘA NE TSAKANINMU ??
Mai bibiyan Rubutu na hakika yasan Wasu Halaye da banbancin zuciyar mace da namiji(musamman a soyayya). Akwai Ɓoyayyen Layi tsakanin Soyayya da Zumunci, Wannan Layi Bai Cika Buya wa mata ba, Amma mu Maza Da yawa Bamu Lura sai yasa mukafi shan wahalar, Misali...
Ita Fa Mace zaku iya zumunci ku Shaƙu Tsawon lkc, zama ka iya jin furuci da Abubuwa sak kmr soyayya amma har zuciya wlh ba soyayya bace😁 duk zumuncin ne kaɗai🙅♂️ a wajenta.
Mu kuma maza musamman Matasa, Dama zuciyar mu kmr Wi-Fi ne kullum searching😄 jin kalma mai dadi ko Ganin Alamun so daga mace baya wuyar Taɓa zuciyar mu.
Tare da cewar ana iya samun Akasi, namiji da shima Zuciyarsa bata fahimtar soyayya da wuri, Wata zata ta nuna masa Alamun so duk ya kasa fahimta, sbd tsammaninsa duk ckn zumunci ne.
Wani Lkcn zaka ga zumunci yayi karfi tsakanin wani da wata, Rana ɗaya sai Su Canzawa juna. Ka rasa dalili, Alhali Ɗaya cknsu ne ya Ƙetara Layin nan na Zumunci Shi kuma Ɗayan hakan ya Ɓata masa Rai😢
ƘALUBALE...
Musamman mu maza, Duk Karfin Zumuncinka da mace karka taɓa Bashi tabbacin zama Soyayya, Dan zuciyarsu Nada Rikici ba dan kaɗan ba😔
Abu ne mai sauki "Inhar kuna zumunci da mace ka Samu zuciyar ta" Amma dan kawai ta sake dakai kwatsam! Ka bijiro da So sai kuma kaga ya zama damuwa, wasu matan Ɗan wannan sai yasa ta tsaneka, karshe zumunci ya lalace💔😢
ckn zumuncinka da kowace mace karka na manta "WACE ALAƘA NE TSAKANINMU" zai Taimakeka ckn Ci gaba da samun yardarta(koda ba soyayya ba). Sannan Ba ina nufin Kai tsaye ka tambaya ba "FAƊA MUN MATSAYI NA A WAJENKI??"🤔 Ko wani abu makamancin haka😄, A'a Ckn Nazari da lura nake nufi. Sai yasa zan temake ka da Wasu Ya'n hanyoyi Na Fahimtar Hakan🤗 Insha Allah👈💯👌
🗣DAGA NAKU MAI SHIN MENE NE SO ✅️ 💘💐