m jaafar said adam rijiyar lemo

m jaafar said adam rijiyar lemo Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from m jaafar said adam rijiyar lemo, Real Estate, yahayaMuhammadumar90agmail. com, Kano.

30/09/2025

Addu'ar shiga Banɗaki:
اللَّهُمَّ إني أعوذُ بك مِنَ الخُبُثِ والخبائِثِ
Bukhari ya ruwaito.

28/09/2025

Addu'ar kwanciya Barci:
بِاسْمِكَ اللَّهُمَّ أَمُوتُ وَأَحْيَا

23/09/2025

“Allah ya shiryar da mutum ɗaya ta dalilinka, ya fi maka alheri fiye da jajayen raƙuma.”
Bukhari da Muslim.

23/09/2025

Ilmin da ba ayin aiki da shi , kamar bishiya ce maras 'ya'ya.
Allah Ka azurta mu da ilmin da za mu yi aiki da shi.

23/09/2025

Hukuncin Sallar Mara Lafiya

Wajibi ne a kan kowane mukallafi — wato mai hankali, wanda ya balaga, kuma saƙon manzoncin Annabi (ﷺ) ya iso gare shi — ya san hukunce-hukunce na sallar mara lafiya. Domin babu wani da aka keɓe daga kamuwa da rashin lafiya.

Sallar farilla tana da halaye bakwai da ake gudanar da ita ta ɗaya daga cikinsu, gwargwadon ƙarfin ikon mai ibada.

Halaye huɗu na farko (wajibi ne a jerenta su):

1. Yin sallah a tsaye, ba tare da jingina da wani abu ba.

2. Yin sallah a tsaye, tare da jingina.

3. Yin sallah a zaune, ba tare da jingina ba.

4. Yin sallah a zaune, tare da jingina.

Wajibi ne mai sallah ya bi waɗannan halaye bisa tsarin da aka jeranta su. Wato, ba ya halatta mutum ya yi sallah da hali na biyu, sai dai idan ya kasa yin hali na farko. Haka nan ba ya halatta ya yi hali na uku, idan yana iya yin hali na biyu. Duk wanda ya tsallake wani hali da zai iya yin sallar farilla da shi, ya koma wani hali na gaba; to sallar sa ta ƁACI.

In sha Allah zamu cigaba da kawo ragowar halayen guda uku, da marasa lafiya za su iya yin ibada da su.

Masjid Bilal Bin Rabah (R.a) (Idrisiyya)

Property

22/09/2025

yasa da Alkhairi malam

22/09/2025

"Mafi Alherin yinin da rana take hudowa a cikinsa shi ne yinin Juma'a"
Muslim ne ya ruwaito.

20/09/2025

"Ku karanta Alkur'ani, domin zai zo ranar Alkiyama ya ceci masu karanta shi"
Muslim ne ya ruwaito.

20/09/2025

"Wanda yake karatun Alkur'ani cikin ƙwarewa yana tare da mala'iku masu girma."

— Imam Muslim.

17/09/2025

Hadisi shi ne duk abin da aka danganta ga Annabi ﷺ — daga maganarsa, aikinsa, ko abin da aka aikata a gabansa bai hana ba.

15/09/2025

Aliyu (R.A) ya ce: “Manzon Allah ﷺ ya yi mini wasiyya: Ba wanda zai so ni sai mumini, kuma ba wanda zai ƙi ni sai munafiki.”
— Sahih Muslim M Sulu

Address

YahayaMuhammadumar90agmail. Com
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when m jaafar said adam rijiyar lemo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category