Community Care Foundation And Initiative CCFI

Community Care Foundation And Initiative CCFI We believe in compassion, action, and sustainable change.

Haske Community Care Foundation (HCCF) is a nonprofit organization dedicated to empowering vulnerable communities through education, health support, and social impact projects.

15/11/2025

Gamayyar gidauniyoyin Arewacin Najeriya sun bukaci attajirai da kungiyoyi su himmatu wajen bayar da taimakon marayu, Zawarawa da marasa galihu a cikin al'umma don kare su daga faɗawa abubuwan da zasu bata tarbiyyar su da zai haifar da matsaloli a cikin al'umma.

Shugaban gidauniyoyin Mal. Sani Rogo Aikawa, wanda kuma shi ne shugaban gidauniyar Aikawa Charity Foundation shi ne ya bayyana haka a ziyarar da gidauniyar Haske Community Care Foundation ta kai masa.

14/11/2025

Haske community care Foundation takai ziyar neman shawarwari da hadin gwiwa da shugaban gidauniyar Aikawa Charity Foundation, Sani Rogo Aikawa.

Sani Rogo ya bayyana farin cikin da wannan ziyara ta aka kawo masa a ranar Juma'a 14 ga Nuwamba 2025.

14/11/2025

Shugaban gidauniyar Haske Community Care Foundation da shugaban gidauniyar Aikawa Charity Foundation Mal. Sani Rogo Aikawa bayan kammala tattaunawa a ranar 14/11/2025.

Aikawa ya bayar da shawawari yadda ake gudanar da gidauniyar tallafawa al'umma, sun hada da dokoki, tsare-tsare, hakuri, juriya, gaskiya da amana.

07/11/2025

Ziyarar da gidauniyar Community Care Foundation And Initiative CCFI (Haske Community Care Foundation ) ta kaiwa shugaban kamfanin Global Venture Nigeria Limited Alh. Hamisu Rabi'u a kasuwar Singa a jihar Kano, ya sha alwashin bayar da gudummawa wajen ci gaba da gudanar da aiyukan alkhairi da kungiyar take yiwa al'umma.

07/11/2025

*🌟 Happy Friday from Haske Community Care Foundation ! 🌟*

As we embrace this beautiful day, we join hands to wish you joy, peace, and purpose.
May your Friday be full of smiles, kindness, and inspiration!

Let’s take today to reflect, to give thanks, and to spread positivity around us.
Together, we move with hope and action.

*Have a blessed Jumu’ah and a joyful weekend ahead!*

05/11/2025

Kadan daga cikin tasirin da gidauniyar Rockefeller Foundation tayi a sassan duniya.
Haduwar kan Al'ummah na'iya haifarda gagarumin cigaban da ita kanta al'ummar batayi tsammani ba.

A tsakanin shekarun 1940s zuwa 1960s, Gidauniyar Rockefeller foundation ta yi babban shiri na tallafawa binciken aikin gona a Mexico da sauran wurare. Wannan ya haifar da Green Revolution, inda aka kirkiro sabbin nau'ukan iri masu saurin girma (musamman masara da shinkafa) da kuma ingantattun hanyoyin noma.
Wannan canjin ya taimaka matuƙa wajen inganta samar da abinci da kuma yakar yunwa a sassan Asiya, Latin Amurka, da wasu sassan Afirka.
Haka a farkon karni na 20, sun ba da tallafi mai yawa don kafa da kuma bunkasa manyan jami'o'i da cibiyoyin bincike a duk duniya, suna mai da hankali kan kimiyya da fasaha.

A halin yanzu, Rockefeller Foundation ta sadaukar da aikinta wajen magance manyan matsaloli na duniya ta hanyar saka jari mai yawa a fannoni huɗu masu mahimmanci, tare da mai da hankali kan sauyin yanayi (climate change):

Makamashi (Power): Taimakawa wajen samar da wutar lantarki mai dorewa (renewable power) ga miliyoyin mutane a Afirka da Asiya, musamman ta hanyar shirin Global Energy Alliance for People and Planet (GEAPP).

Lafiya (Health): Inganta tsarin kiwon lafiya na duniya da kuma amfani da sabbin fasahohi don shirya wa annoba ta gaba.

Abinci (Food): Tallafawa Noma Mai Dorewa (Regenerative Agriculture) da kuma tabbatar da cewa mutane suna samun abinci mai gina jiki mai sauki a duniya.

Kuɗi (Finance): Amfani da hanyoyin kuɗi daban-daban don jawo hankalin masu saka hannun jari don tallafawa ayyukanta.

Community Care Foundation And Initiative CCFI .

02/11/2025

Haske Community Care Foundation visited one of the father of this Organization Alh. Hamisu on yesterday 01 Nov 2025.

Thanks you for our welcoming.

02/11/2025
01/11/2025

Haske Community Care Foundation Ta Kai Ziyarar Girmamawa Ga Mai Martaba Sarkin Hausawan Afirka

Daga Ibrahim Idris Abdullahi (Danbaba)

Gidauniyar Haske Community Care Foundation ta kai ziyarar girmamawa ta musamman zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Afirka, Ambassador Alhaji Abdulƙadir Labaran Koguna, da ke unguwar Yola a Jihar Kano, domin neman shawarwari da haɗin kai a matsayinsa na uba ga al’umma.

Ziyarar ta gudana ne a ranar Laraba, 29 ga Oktoba, 2025, karkashin jagorancin shugaban gidauniyar, Malam Ahmad Adamu.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Malam Ahmad Adamu ya bayyana cewa manufar zuwansu ita ce gaisuwar ban-girma da neman shawarwari daga Mai Martaba Sarki a matsayin jagoran al’umma.

Ya kuma bayyana cewa babban maƙasudin kafa gidauniyar Haske Community Care Foundation shi ne wayar da kan al’umma a fannoni da dama, ciki har da tsaro, ilimi, lafiya, tallafawa marasa galihu, da kuma yaƙar yaduwar miyagun ƙwayoyi da sauran matsalolin da ke hana ci gaban al’umma.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Hausawan Afirka, Ambassador Alhaji Abdulƙadir Labaran Koguna, ya nuna matuƙar farin ciki da wannan ziyara mai albarka, tare da yabawa ƙoƙarin gidauniyar wajen ayyukan alheri da taimakon jama’a.

Ya ce “Ina tare da ku, kuma zan ci gaba da bayar da shawarwari domin gidauniyar ta samu cigaba, don ganin an samu zaman lafiya da yalwar arziki.”

Haka kuma, Mai Martaba ya ƙara ba da shawara kan muhimmancin wayar da kai ga al’umma da ƙwazo wajen aiki tuƙuru, domin cimma nasarorin da gidauniyar ta sanya a gaba.

Ya kuma bukaci su riƙa martaba yaren Hausa da al’adunsa, tare da riƙo da gaskiya da amana kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

Sarkin Hausawan Afirka ya kuduri aniyar bayar da duk wata gudunmawar da ake buƙata domin taimakawa wajen tafiyar da ayyukan gidauniyar don ci gaban al’umma.

A ƙarshe, shugaban gidauniyar, Malam Ahmad Adamu, ya nuna farin cikinsa da irin kyakkyawar tarba da Sarkin ya yi masu.

Ziyarar ta samu halartar wasu daga cikin manyan mambobin ƙungiyar, ciki har da:

Hajiya Fatima Hassan Sa’id – mataimakiyar shugabar gidauniya

Abdulshakur Umar – Sakatare

Ibrahim Idris (Danbaba) – Ma’ajin kuɗi

Saifullahi Auwal – Mai haɗin kai ga al’umma

Adam Sa’id Adam – Jami’in hulɗa da jama’a

Hussaina Hassan Bako - mamba

Haske Community Care Foundation (HCCF) Pays Courtesy Visit to His Royal Highness, the King of Hausa AfricaBy AARThe Comm...
31/10/2025

Haske Community Care Foundation (HCCF) Pays Courtesy Visit to His Royal Highness, the King of Hausa Africa

By AAR

The Community Care Foundation and Initiative (CCFI) has paid a courtesy visit to His Royal Highness, the Sarkin Hausawan Afrika, Sardaunan Agadez, Ambassador Dr. Abdulkadir Labaran Koguna, at the Emirate Palace in Yola, Kano State. The visit, held on Wednesday, October 29, 2025, was aimed at seeking royal blessings and support for the foundation’s ongoing community development initiatives.

The delegation, led by the foundation’s chairman, Comrade Ahmad Adamu, included key members of the organization.

In his address before His Royal Highness, Comrade Ahmad Adamu highlighted that the foundation was established to serve as a catalyst for community development, humanitarian assistance, and public awareness, especially in the areas of education, health, and security.

Ahmad Said “Our major focus includes organizing awareness campaigns, supporting underprivileged children and youth, and implementing various humanitarian and community development programs,” he said.

Responding, His Royal Highness, Dr. Abdulkadir Labaran Koguna, commended the foundation for its dedication to the welfare of society. He emphasized the importance of preserving the Hausa language and culture, urging members to remain steadfast and sincere in their mission.

The monarch further assured the delegation of his continued support and cooperation in advancing the foundation’s objectives.

In closing, Comrade Ahmad Adamu, on behalf of the delegation, expressed profound gratitude to His Royal Highness for the warm reception and encouragement. He reaffirmed the foundation’s commitment to promoting Hausa culture and upholding the principles of truth and trustworthiness as advised by the King.

Those in attendance included:

Hajiya Fatima Hassan Sa’id – Vice President, Abdulshakur Umar – Secretary, Ibrahim Idris (Danbaba) – Treasurer, Saifullahi Auwal – Organize Secretary, Adam Sa’id Adam – Public Relations Officer, Hussaina Hassan Bako – Member

Community Care Foundation And Initiative CCFI

Address

BUK Road
Kano
BUKLINK12,JANBULOKABUGA,GWALELGA,KANOSTATE,NIGERIA.

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Community Care Foundation And Initiative CCFI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category