17/10/2026
KAI JAMAA
wannan Gidan fa 270k muka Bada shi Haya a 2024 Amma kun San cewa gidajen 600k a yanzu basa kaishi Kyau da GIRMA???
Muna Kira da Masu Gidajen Haya suyiwa Allah suyiwa soyyyar maaiki S.A.W su sauke farashin Gidajen Haya.
wallahi tsadar tayi yawa, Babu dadii ko kadan.
Don Allah a sauke farashin Gidajen Haya ko jamaa zasu samu saukin Kara Aure Inda su Kuma Samari zasu samu damar yin Auren Fari.
Don Allah mu saukaka.
Zan baku misali da ni kaina a matsayin dillalin Gidajen SAYARWA da na Haya, A sati uku da ya wuce akwai Wanda ya sayi Gida a wajena, sai Yace Malam Abdullahi don Allah kayiwa gidannnan kudin Haya sai nace Masa zamu Iya karbar 450k ko 500k highest 550k duk shekara, Sai Yace aa Saka shi A 700k sai nayi shiru domin nasan shi baisan darajar Haya a Unguwar bane, saboda shi Yana babbar unguwa ne kaga kila yayi comparing da Unguwar sa ne, wallahi cikin hikima sai da na bashi shawara aka dawo dashi 600k, da yake mutumin kirki ne Mai mutunci da karamci ya yarda Yace babu komai Allah ya saukaka mana, kwatsam sai ga Mai kamawa Yana matukar son Gidan Amma Yace abinda zai Iya biya cikin sauki duk shekara shine 550k, wallahi da na kirashi nace Masa a duba matsin Rayuwa da Ake ciki wallahi sai ya yarda Yace babu komai a karba.
Tabbas, mutumin kirki ne, Allah yasaka Masa da alkhairi. yakaro Irin su a cikin alumma
Naku Abdullahi Garba 07038276756