01/05/2024
DALILAI NA HADISI MASU NUNA
CEWA IYAYEN ANNABI (SAW)
'YAN ALJANNA NE.
Sheikh Halliru Abdullahi Maraya Kaduna.
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT)
da Ya ba mu dama , a jiya , muka
gabatar da wasu daga cikin dalilai
na hankali masu nuna cewa iyayen
Manzon Allah (SAW) ba 'yan wuta
ba ne . Allah (SWT) Ya kara masu
(AS)
rahama da yarda . In sha'Allah ,
yau , zamu kawo wasu dalilai na
Hadisin Manzon Allah (SAW) masu
nuna haka .
Allah (SWT) Ya kara wa ManzonSa
(SAW) matsayi da alfarma . Akwai
dalilai na Hadisin Manzon Allah
(SAW)
da suke nuna cewa iyayensa (AS)
muminai ne , 'yan
Aljanna . Daga ciki akwai :
i. Waathilah Ibnu Asqa'i (RA) ya
ce : Manzon Allah (SAW) ya ce "
Lallai Allah Ya zabi Ismaa'iil (AS)
daga cikin 'ya'yan Ibraahiim (AS) ,
kuma Ya zabi 'ya'yan Kinaanah
daga cikin 'ya'yan Ismaa'iil (AS) ,
kuma Ya zabi Quraysh daga cikin
'ya'yan Kinaanah , kuma Ya zabi
'ya'yan Haashim daga cikin
Quraysh , sannan (daga karshe)
Ya zabe ni daga cikin 'ya'yan
Haashim ."
Manazarta : Sahiihu Muslim .
ABUN DA HADISIN KE NUNAWA :
Wannan Hadisi yana nuna cewa a
cikin kowace Jama'a , tun daga
Annabi Ibraahiim (AS) har zuwa
lokacin haihuwar Manzon Allah
(SAW) , Allah (SWT) Yana zaben
mutane ne mafifita a wurinSa
(SWT) , sannan Ya sa Manzon
Allah (SAW) a tsatsonsu .
A takaice , mai lafiyayyen hankali
zai fahimta daga wannan Hadisi
cewa iyayen Manzon Allah (SAW) ,
tun daga Annabi Ibraahiim (AS)
zuwa iyayensa na haihuwa ,
zababbu ne a wurin Allah (SWT) .
Kafirai kuwa ba zababbu ba ne a
wurin Allah (SWT) . Saboda haka ,
Hadisin ya nuna cewa Abdul-Laahi
(AS) da Aaminatu (AS) , iyayen
Manzon Allah (SAW) , zababbu ne
a wurin Allah (SWT) ba 'yan wuta
ba .
ii. Sayyidunaa 'Aliyyu (RA) ya ce :
Manzon Allah (SAW) ya ce : " An
haife ni ne ta hanyar aure , ba a
fitar da ni ba ta tsatson mazinaci
tun daga Aadam (AS) har zuwa
lokacin da mahaifina da
mahaifiyata s**a haife ni ."
Manazarta : Imam At-
Tabaraaniyyu , Mu'jamul-awsad .
ABUNDA HADISIN KE NUNAWA :
Wannan Hadisi na nuna cewa
iyayen Manzo