Yahya Nuhu Sallau -Khalifa

Yahya Nuhu Sallau -Khalifa Informations de contact, plan et itinéraire, formulaire de contact, heures d'ouverture, services, évaluations, photos, vidéos et annonces de Yahya Nuhu Sallau -Khalifa, Immobilier, Diffa.

26/02/2026
06/01/2026

TARIHIN KHALIFA SHEIKH YAHYA NUHU SALLAU

SUNA:
Yahya Nuhu Sallau.

Sallau lakabine da hausawa suke yiwa duk wanda aka haifa a ranar idin azumi ko layya, amma sunansa Hasan.

MAHAIFI:
Nuhu dan Sallau dan Salihu dan Muhammadu.
Sunan mahaifiyarsa Hajara. (1934 - 1997)

MAHAIFIYA:
Halimatu 'yar Sani Kafanga dan Hasan dan Muhammadu dikko dan Ahmad dan Ahmad.
Sunan mahaifiyarta Safiyyatu. (1952 tana nan a raye).

HAIHUWA:
Ranar alhamis 28 ga watan Safar shekarar hijira 1389.
Daidai da 15 ga watan Mayu shekarar miladiyya 1969.

WURIN HAIHUWA:
Unguwar Dausayi a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Gwale a cikin jihar Kano.

KARATUN ZAMANI:
1- Goron dutse Primary school 1976 - 1982.
2- Goron dutse secondary school 1983 - 1986
G.A.T.C Gwale 1986 - 1990
3- B.A a harshen larabci daga Islamic University in Niger 1993 - 1997.

KARATUN ADDINI
Ya yi karatun:
Fikhu.
Hadisi.
Tafsir.
Nahwu.
Luga.
Sufanci.
A wurin mahaifinsa

AYYUKA;
2- Ya Khalifanci mahaifinsa bayan rasuwarsa yana da kimanin shekaru ashirin da takwas. A cikin dukkan harkokin karantarwarsa.
2- Ya yi aikin koyarwa a karkashin hukumar kula da ilimin firamare daga 1990 – 2006.
3- Ya zama mai fassara hudubar liman a masallacin Sheikh Muhammadur Rabi’u (R.A) na Khalifa Sheikh Is’haku Rabi’u (R.A) daga 1997 – 2002.
4-Ya rike matsayin limami ratibi a masallacin Sheikh Ahmadut Tijani (R.A) na Khalifa Sheikh Is’haku Rabi’u (R.A) daga 2002 – 2007.
5- A yanzu shine mataimakin sakataren ilimi na Munazzamatu fityanil islami na kasa baki daya.

AURE DA 'YA'YA;
Ya auri Aminatu Sharif Danlami maikwano ta haifi:
1- Fadimatu.
2- Khadijatu.
3-A'ishatu.
4- Halimatu (Sharifa).
5- Muhammadu (Maulaya).
Ya auri Fadimatu Yahya ta haifi:
6- Ahmad
7- Mahmud.

DARIKA:
Ya karbi darika a wurin Sheikh Sani Kafanga (R.A) a shekarar 1986.

TARBIYYA:
Ya yi tarbiyatul azkar a wurin Sheikh Mahmud Salga (R.A) a shekarar 1989.

TAKDIMI;
Ya sami izini mudlaki daga wurin Sheikhunai da yawa daga cikinsu akwai.
1- Sheikh Abdullahi dan Sheikh Ibrahim Niasse (R.A.H) daga mahaifinsa.
2- Sheikh Shu'aibu Niamey (R.A) daga Sheikh Ibrahim Niasse (R.A).
3- Sheikh Aliyyu Harazimi (R.A) daga Sheikh Gibrima (R.A).
4- Sheikh Sharif Danlami maikwano (R.A) daga Sheikh Abdurrazzaki Kusa (R.A).

RUBUCE RUBUCE;
Ya rubuta littattafai da yawa a harshen larabci da na hausa, na yiwa wasu littattafan da aka rubuta su da larabci sharhi ko rataye ko tahkiki, ya kuma fassara wasu zuwa harshen hausa, yana da rubutattun wakoki a harshen larabci da na hausa.

RUBUTU:
1-مرآة التجاني
2- التبديع أخطر بدعة تتخلل صفوف المسلمين.
3- أيها الزوجان
4- التشاعريات.
5- مجربات الصلوي.
6- القريض الوافي في العروض والقوافي.
7- المعيار في أوزان الأشعار.
8- من أبياتنا.

9- Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi wa sallama kamar kana ganinsa.
10- Tarihin rayuwar Sheikhu Ahmadut Tijani (R.A) kamar kuna tare.
11- Gyara kayanka.
12- Madubin Tijanawa.
13- Kwance kullin karkiya.
14- Wakokina.

FASSARA;
1- Alkur'ani mai girma.
2- Diwani
3- Ruhul adabi
4- Conakriyya.
4- Hasbil muhaiminu.
5- Annurur rabbani.

RATAYE KO SHARHI;
1- تعليقات على قصائد المولد النبوي
2- رفع الرتب في شرح روح الأدب.
3- الفتح النوراني في شرح النور الرباني.
4- نيل الوطر على نور البصر .

TAHKIKI:
1- غاية الأماني في سيرة أحمد التجاني.
2- سبيل السلام في إبقاء المقام.

ZABINSA:
Babban abin da ya fi sha’awa shine karance karance da rubuce rubuce da bincike a cikin fannonin ilimai mabanbanta.
Yna son zaman kadaici da tafiye tafiye da kallon fina finai, ba shi da aboki na k*t da k*t, ba ya son zama a karkashin wani.
Mafi yawan aiyukan da ake yi a lokacin kuruciya bai aikata su ba kamar:
Kwallon kafa
Wanka a ruwa.
Da makamancin haka.
Ba ya son karya da yaudara da saba alkawari.

BURINSA:
1- Ganin Sayyidul wujudi Sallallahu alaihi wa sallama a zahiri da zuwa ziyararsa.
2- Mutuwar shahada a cikin daukaka addinin Allah Ta'ala.
3- Wadatuwa ga barin dukkan abin halitta.

Allah ya kyautata halittarmu da dabi'armu. Amin.

20/12/2025

Allah! Ka kiyaye mu daga matsalolin jahilan maƙiya da wawayen masoya.
Sallawi ke magana.

19/12/2025

Ya Allah ka kiyaye almajiran Sheikh Tijani Radhiyallahu anhu daga sharrin Shaikhunan mimbari da wautar Shaikhunan social media!.
Sallawi ke magana.

26/11/2025

Duk Shaikhin da yace sai ka rabu da Shaikhinka zai yi maka tarƙiyya! Ɗan damfara ne.
Haka kuma duk Shaikhin da ya hana ka yin tarƙiyya! Maha'inci ne.

Sallawi ke magana.

Adresse

Diffa

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Yahya Nuhu Sallau -Khalifa publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Partager