First Aid Group fityanul Islam codasu unit

20/01/2026

HIGHLIGHTS OF FITIYANUL ISLAM IN NUMAn adamawa

Silencing the Voice of Scholarship: The Unjust Incarceration of Sheikh Sani Khalifa of ZariaBy Dr. Zanna Hassan Boguma F...
06/01/2026

Silencing the Voice of Scholarship: The Unjust Incarceration of Sheikh Sani Khalifa of Zaria

By Dr. Zanna Hassan Boguma FCIPDM FWIP
(Zanna Boguma of Borno)

In a nation already burdened by insecurity, economic hardship, and a crisis of trust between citizens and the state, the abduction and continued incarceration of Sheikh Sani Khalifa of Zaria stands as a troubling symbol of misplaced priorities and dangerous injustice. Sheikh Sani Khalifa is not a fugitive, a militant, or a public menace. He is a renowned Islamic scholar, a teacher of the Qur’an, and a spiritual guide to hundreds of students and disciples, many of them ḥuffāẓ, memorizers of the Noble Qur’an, whose lives have been shaped by his learning, discipline, and moral counsel.

Yet today, his whereabouts and conditions remain unknown to his family, followers, and students. There has been no transparent charge, no public arraignment, no due process that a democratic society claims to uphold. What circulates instead are disturbing reports on social media suggesting that Sheikh Sani Khalifa was taken into custody following the discovery of a certain sum of money in his bank account. If true, this explanation is not only inadequate, it is an affront to justice.

Nigeria is a country where well-documented allegations of monumental corruption, running into billions, have been leveled against public officials and power brokers, many of whom continue to walk freely, enjoy state protection, and even receive political patronage. Known criminals are escorted, rehabilitated, and negotiated with. Some are rewarded with amnesty; others are absorbed into the very structures meant to hold society together. Against this backdrop, the targeting of a religious scholar over an unspecified amount of money reeks of selective justice and institutional hypocrisy.

Justice cannot be credible when it is harsh on the weak and gentle with the powerful. It cannot command respect when scholars are seized in the dark while looters of public wealth dine in the open. And it cannot sustain peace when moral authorities are humiliated without cause, process, or explanation.

Beyond the legal and moral outrage lies a deeper danger: it is politically and socially suicidal to wage war against religious leaders, especially those with deep roots in their communities. Scholars like Sheikh Sani Khalifa are not mere individuals; they are institutions of learning, symbols of restraint, and anchors of social order. They command loyalty not through force, but through knowledge, piety, and service. To persecute such figures unjustly is to risk alienating entire communities, eroding trust, and sowing seeds of resentment that no security apparatus can contain.

History, Nigeria’s included, teaches us that when states criminalize moral voices and silence scholars, they do not strengthen themselves; they weaken. They create martyrs where none need exist. They turn disagreement into grievance, and grievance into instability.

If there are genuine questions regarding Sheikh Sani Khalifa’s finances, the law provides clear, humane, and transparent procedures: invitation, investigation, charge, and fair trial. Abduction, incommunicado detention, and secrecy are not tools of justice; they are markers of fear and failure.

We therefore call for the immediate and unconditional release of Sheikh Sani Khalifa of Zaria. Anything short of this is a continued violation of his rights and a stain on the conscience of the nation. Furthermore, a public apology is owed, to the Sheikh himself, to his family who have been plunged into anguish, and to his followers and students whose trust has been shaken and whose learning has been interrupted.

Nigeria does not need more enemies within. It needs bridges of trust, equity before the law, and respect for institutions, religious, civic, and scholarly, that hold society together. Silencing Sheikh Sani Khalifa will not solve corruption. It will not bring security. It will only expose the tragic contradiction of a system that spares the corrupt and punishes the righteous.

Let justice be done, not selectively, not secretly, but openly, lawfully, and courageously.

*📸JUMMA'AT MUBARAK📸*        Muna Mika SakonBarka Da Jumma'a A Madadin _*Maj.Gen.Alh. Ibrahim Shuaibu Suddu (S.s Zaria)*_...
02/01/2026

*📸JUMMA'AT MUBARAK📸*

Muna Mika Sakon
Barka Da Jumma'a A Madadin _*Maj.Gen.Alh. Ibrahim Shuaibu Suddu (S.s Zaria)*_

👏🏻Zuwa Ga Musulmin Duniya 💞

🤲بسم الله الرحمن الرحيم 🤲

*اللهم صل وسلم على نبينا محمد ﷺ*

"Barkan Mu Da Jumma'a,

Karda Mu Manta Da Karanta Suratul Kahfi A Ranar Jumma'a

🤲Alhamdulillah 🤲🏼

"Babbar dukiyar ɗan Adam ita ce kyawawan halayensa waɗanda ke ƙawata rayuwarsa da inganta halayensa,

Allah ya sa mu dace, ya cika rayuwarmu da albarka.

*💞Bijahi Mustaphal Kareem💞!*

_🌹Jumma’at Mubarak 🌹_

*💻 Media & Publicity*
_Office of the National Parade & Decoration, FAG 2/01/2026._

TA’AZIYAInnalillahi wa'innah ilahi rajiu'n 😭A madadin Maj. Gen. Alh. Ibrahim Shuaibu Suddu (SS Zaria), muna miƙa sakon t...
01/01/2026

TA’AZIYA

Innalillahi wa'innah ilahi rajiu'n 😭

A madadin Maj. Gen. Alh. Ibrahim Shuaibu Suddu (SS Zaria), muna miƙa sakon ta’aziya da alhini mai zurfi ga Malam Ismail Aliyu Tanti, North Central Zonal Admin na FAG, bisa rasuwar😭 ’ya’yan yayarsa guda shida (6) da s**a rasu sakamakon gobarar wuta,🔥 Wannan lamari abin tausayi ne matuƙa, kuma ya girgiza zukatanmu baki ɗaya.

🙏Muna roƙon Allah Ya ba mahaifiyarsu da ke kwance a asibiti lafiya

🤲Muna addu’ar Allah (SWT) Ya jikansu da rahama.

💻 Media & Publicity
_Office of the National Parade & Decoration, FAG 01/01/2026._

Gwamnati Ta Kammala Horar da Sama da Matasa 7,000 a Matsayin Masu Tsaron Daji Da Za a Tura su Aiki Nan takeGwamnatin Tar...
27/12/2025

Gwamnati Ta Kammala Horar da Sama da Matasa 7,000 a Matsayin Masu Tsaron Daji Da Za a Tura su Aiki Nan take

Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala horar da fiye da matasa 7,000 da aka dauka a matsayin Masu Tsaron Daji (Forest Guards) a jihohi bakwai da ake ganin suna fuskantar matsanancin barazanar tsaro.

Wannan horo ya gudana ne karkashin shirin Presidential Forest Guards Initiative da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya kaddamar a watan Mayu na shekarar 2025 domin dawo da ikon gwamnati a cikin dazuzzuka da ke kara zama mafakar 'yan ta'adda, 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.

An gudanar da bikin yaye daliban a ranar 27 ga Disamba, 2025 a jihohi Borno, Sokoto, Yobe, Adamawa, Niger, Kwara da Kebbi, inda kowane bangare na horon ya kasance mai tsauri da tsari, domin gina dakaru masu kwarewa da jajircewa wajen aikin cikin daji da wuraren da ba a iya shiga cikin sauki.

A bayanin da ya gabatar a bikin yaye su, Mai Ba Da Shawara kan Tsaron Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana shirin a matsayin “mataki mai karfi” wajen dawo da zaman lafiya da kare al’ummomi.

“Wadannan Masu Tsaron Daji ba kawai ma’aikata bane da s**a sa kaya. Su ne masu kare al’umma, masu tarin bayanai, kuma ginshiki a cikin tsarin tsaronmu. Za su tsaya a kasa, su wanke wuraren da masu aikata laifi ke buya, su kuma taimaka wa jami’an tsaro wajen kwato yankunan da miyagu s**a mamaye,” in ji shi.

Ya kara da cewa, babu wani tazara tsakanin kammala horo da fara aiki:
“Nan da nan za a tura su bakin aiki, albashinsu da hakkokinsu za su fara nan take.”

An shafe watanni uku ana horar da wadanda aka dauka, inda aka mayar da hankali kan:

Horon jiki da kwakwalwa (physical & mental endurance)

Tsallake cikas, da hanyoyin jure doguwar tafiya cikin daji

Horar da su kan dabarun yaki da tsari na tsaro (tactical drills)

Horo kan mayar da martani yayin farmaki, da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su

Horon kyakkyawar mu’amala da fararen hula, kare hakkin bil’adama, da bin doka

Daga cikin wadanda s**a halarta horon, kashi 98.2 cikin ɗari ne s**a kammala. An kori mutane 81 sakamakon kin bin ka’ida, yayin da biyu s**a rasu saboda matsalolin lafiya. Mafi yawansu ’yan asalin yankunan da za su yi aiki ne, abin da gwamnati ta ce zai taimaka musu wajen sanin daji, hanyoyin shiga da fita, tare da samun goyon bayan al’umma.

Masu Tsaron Dajin na karkashin kulawar Ofishin Mai Bada Shawara kan Tsaron Kasa tare da Ma’aikatar Muhalli, karkashin daidaitawar DSS da Hukumar National Park Service. Haka kuma rundunar soji, rundunar sojin ruwan Najeriya, rundunar ’yan sanda da NSCDC duk sun bayar da gudummawa wajen tsari da dabarun aiki.

Gwamnoni da mataimakansu daga jihohin da abin ya shafa sun halarci taron, ciki har da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yayin da wasu jihohin s**a samu wakilci daga mataimakan gwamnoni.

A karshe NSA Nuhu Ribadu ya sake jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da fadada shirin zuwa sauran jihohi:

“Idan muka kare dazukanmu, mun kare kasa. Idan muka kare kasa, mun kare rayukan al’ummanmu. Gwamnatin Tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba.”

15/12/2025

Zuwan shugaban kungiyar Fityanul Islam of nageria na kasa shek Muhammad Arabi Ahamad Abulfathi ta'aziyya gidan shek dahiru usman bauchi Allah yakara masa rahma

Labarin fim din zai farfado da ilmin 'ya'ya mata a Arewacin Nijeriya, hada kai da kaso zaman lafiya a kasa, in ji mai sh...
26/11/2025

Labarin fim din zai farfado da ilmin 'ya'ya mata a Arewacin Nijeriya, hada kai da kaso zaman lafiya a kasa, in ji mai shirya fim din

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’adu Abubakar III, tare da Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Nijeriya sun bayar da cikakkiyar amincewa ga kamfanin Script Plus Limited karkashin jagorancin Rahma Abdulmajid domin fara aikin shirya fim kan rayuwa da bajintar Nana Asma’u, fitacciyar malama, mawallafiya kuma mai fafutukar ilimi a karni na 19.

Fim ɗin zai nuna gudummawar da Nana Asma’u, diyar Shehu Usman Ɗan Fodiyo, ta bayar wajen ilmantarwa, karfafa mata da gina ilimin addini, tare da ba da gudummawa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin Nijeriya.

A wata wasiƙa mai dauke da kwanan wata 21 ga Nuwamba 2025, Sarkin Musulmi ta hannun Sakataren Majalisar Sarautar Sokoto, Sa’idu Muhammadu Maccido (Danburam Sakkwato), ya bayyana cikakkiyar amincewar majalisar ga aikin fim din da Rahma take jagoranta.

Wasiƙar ta ce, “Mun yi farin ciki da wannan yunkuri na shirya fim kan Nana Asma’u bnt. Usman bn. Fodiyo, wadda a wurin mutane da dama ita ce sahihin misalin mata Musulmi a Afirka. Majalisar Sarautar Sakkwato na bayyana amincewa da wannan aiki kuma muna ba ku izinin farawa kamar yadda kuka nema.”

A nata bangaren, Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya ta bayar da takardar shaidar rijistar tambarin alamar kasuwanci (trademark) na aikin, wanda hakan ke nuna cikakken goyon bayanta.

Da take karin haske kan aikin, Hajiya Rahma Abdulmajid ta ce amfanin fim din, ba wai zai tsaya a iya Arewacin Nijeriya ba, zai kuma nishadantarwa da ba da tarihi, haka kuma zai inganta hadin kai da kaunar juna a tsakanin 'yan kasa.

Ta ce “Wannan labari ne na jagoranci, tsoron Allah da neman ilimi, labari ne da ya shafi dukkan ‘yan Nijeriya. Manufar mu ita ce mu nuna irin ginshikin da mutanen da s**a gabace mu s**a kafa, domin wannan gadon al’adu ya kasance hanyar hada kan Hausawa, Fulani da sauran kabilu a Nijeriya.”

Game da tasirin labarin ga ilimin mata a Arewa, Hajiya Rahma ta ce rayuwar Nana Asma’u hujja ce ta tarihi cewa ilimin mata tushensa yana cikin al’adar Arewa da addinin Musulunci, ba wani sabon abu daga waje ba.

Ta kara da cewa “Rayuwar Nana Asma’u ta tabbatar da cewa ilimin mata al’ada ce a wannan yanki, kuma wani bangare ne na darajar addini da al’adunmu. Ba wani sabon tunani daga Yamma ba.”

Ta ce nuna irin ilimin da Nana Asma’u ta yada zai taimaka wajen karya tunanin cewa karatun mata sabuwar al’ada ce da ba ta dace da yankin Arewa ba.

A cewar ta, rashin ilimi na haifar da rauni a zamantakewa, rashin bin addini yadda ya kamata, tsattsauran ra’ayi da kuma amfani da mata wajen siyasa.

“Nana Asma’u madubi ce da za mu kalla don mu ga gaskiya. ilmantar da mata Arewa komawa ne ga gadonsu, ba saba wa al’adar su ba,” in ji Hajiya Rahma Abdulmajid.

12/11/2025
SHUGABAN FITYANUL ISLAM RESHEN BABBAN BIRNIN TARAYYA ABUJA IMAM Murabbi Mustapha-Kadai ALBARNAWY YA KARBI BAQUNCIN SHUGA...
12/11/2025

SHUGABAN FITYANUL ISLAM RESHEN BABBAN BIRNIN TARAYYA ABUJA IMAM Murabbi Mustapha-Kadai ALBARNAWY YA KARBI BAQUNCIN SHUGABAN NUSRET, MR. HUSEYIN SELVI NA QASAR TURKIYA (TURKISH)

A yau Laraba 12 ga watan Nuwanba, shugaban kungiyar Fityanul Islam reshen Abuja ya karbi Bakuncin Shugaban Nusret Educational and Cultural Co. Ltd. Nigeria. Na kasa baki daya Mr. Huseyin Selvi. A offishin Qungiyar Fityanul Islam reshen Abuja dake No 11 Ajesa street Wuse 2 Abuja.

A cikin ganawar tasu Shugaban na Nusret ya qaddamar da takarda ga Shugaban Fityanul Islam reshen Abuja, Imam Murabbi Mustapha Kadai Albarnawy wacce take dauke da neman hadin guiwar sa wajen shirya Workshop na kwana daya (One day workshop) a nan Babban birnin tarayya Abuja.

Tuni dai Ba tare da bata lokaci ba Shugaban Fityanul Islam reshen Abuja Imam Murabbi Albarnawy ya bada hadin kai da amincewa da wannan qudurin

Yayinda Shugaban nin guda biyu s**a Umarci mataimakan su da membobin su da su fara Shirye Shiryen gudanar da wannan workshop din na kwana daya

Zaman ya samu halartar Jagoririn Fityanul Islam reshen Abuja bangaren Uwar kungiya dana Agaji Kamar Ameera Sayyida Rukayya Sheikh Umaru Sanda, Alhaji Gambo Ngulak, Malam Ibrahim Shu'aibu Suddu, Malam Yusuf Dahiru Abubakar, Malam Mukaffa Ibrahim Malam Atiku Zuba da sauran su.

Sanarwa daga Mukaffa Ibrahim
P.R.O Fityanul Islam Abuja Branch.

12/11/2025

Taimakon Farko Bayan Karaya Kafin Garzayawa Asibiti.A yayin ka zo kan mutum domin bayar da taimakon farko bayan afkuwar ...
04/11/2025

Taimakon Farko Bayan Karaya Kafin Garzayawa Asibiti.

A yayin ka zo kan mutum domin bayar da taimakon farko bayan afkuwar wani iftila'i kamar haɗarin abin-hawa, faɗuwa, faɗowa, ta'addanci ko rushewar gini sannan ka lura ya samu karaya a hannu ko ƙafa, to akwai matakai uku da ya kamata ka bi game da karayar kafin zuwa asibiti.

Matakan sune kamar haka:

1. A tsayar da zubar jini idan buɗaɗɗiyar karaya ce. Buɗaɗɗiyar karaya ita ce karayar da ƙashi ya karye sannan ya fasa nama da fata har ya fito waje. Za a iya tsayar da zubar jini ta hanyar dannewa ko naɗewa da mayani ko ƙyalle mai tsabta. Kada a yi ƙoƙarin daidaita ƙashin da ya karye. Domin hakan na iya raunata jijiyoyin jini ko jijiyoyin laka da ke wurin.

2. A tallafi karayar ta hanyar amfani da kara ko itace a gefe da gefe sannan a ɗaure domin hana karayar motsi.

3. A sanya ƙanƙara tsawon minti 20 a wurin karayar domin rage kumburi, raɗaɗin ciwo da zubar jini. Ya kamata ƙanƙarar a farfasa ta sannan a ƙunshe ta cikin zani ko tawul mai tsabta. Kada a ɗora ƙanƙara kai tsaye a kan fata.

Ɗaukar waɗannan matakai zai taimaka kiyaye matsaloli kamar rage zubar jini, kiyaye shigar ƙwayoyin cutuka, kiyaye lahani ga tsokoki, jijiyoyin jini, jijiyoyin laka ko kuma ƙara ta'azzara karayar.

Da zarar an kammala ɗaukar waɗannan matakai uku, to lokacin garzayawa zuwa asibiti ya yi.

Ibrahim shuaibu suddu NATIONAL parade and decorations First Aid group fityanul islam of nageria

*SAKON GARGADI ⚠️*An lura da yadda wasu ke amfani da (AI) wajen wallafa rank, baji, da sauran abubuwa na kungiyar ba bis...
18/10/2025

*SAKON GARGADI ⚠️*

An lura da yadda wasu ke amfani da (AI) wajen wallafa rank, baji, da sauran abubuwa na kungiyar ba bisa ka’ida ba. _*Ofishin National Parade and Decoration*_ yana gargadi tare da jan kunne cewa kada wani ya sake amfani da (AI) wajen haɗa rank, baji, ko sauran kayan kungiyar *Agajin Fityanul Islam* ba tare da izini ba.

Don haka, _*ofishin tsare-tsare da kula da Uniform na Ƙasa (National Parade and Decoration – FAG)*_ yana gargadi cewa duk wanda ya sake yin amfani da sunan ko tambarin ofishin ba bisa ka’ida ba, za a miƙa shi kai tsaye zuwa ga *Kwamitin Ladabtarwa na Ƙasa* domin ɗaukar mataki.

Doka tana da hakki, kuma ladabtarwa tana kare mutuncin ofishin da tsarin kungiyar Fityanul Islam of Nigeria.

*Abi doka a kiyaye dokokin kungiyar don a zauna lafiya!*

*💻 Media & Publicity*
_Office of the National Parade & Decoration, FAG 18/10/2025_

Address

NO 11 Dantata Estet Kubwa Fct Abuja
Abuja
CODASU67774670SSXARIA

Telephone

+2347067774670

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when First Aid Group fityanul Islam codasu unit posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to First Aid Group fityanul Islam codasu unit:

Share

Category