Nigerian News

Nigerian News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nigerian News, Real Estate, Madalla, Abuja.
(1)

Jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya bayyana hakan bayan ganawa da masu ruwa da tsaki na tafiyar Kwankwasiyya rana...
03/01/2026

Jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya bayyana hakan bayan ganawa da masu ruwa da tsaki na tafiyar Kwankwasiyya ranar Juma'a.

Kwankwaso ya kuma yi kira ga mabiyansa su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai a wannan lokaci.

Amurka ta fara Luguden Wuta a Ƙauyukan Musulmi dake Jabo a Sokoto.Mutanen garin Jabo da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a ji...
26/12/2025

Amurka ta fara Luguden Wuta a Ƙauyukan Musulmi dake Jabo a Sokoto.

Mutanen garin Jabo da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto sun tsunduma cikin firgici a daren Alhamis, ranar bikin Kirsimeti, bayan jin karar saukan Luguden bamabamai a Yankin.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne kwatsam, inda wani abin da ake zargin ya yi k**a da bam ya faɗo cikin al’umma. Abin farin ciki, ba a samu asarar rai ba, domin na’urar ba ta fashe a cikin taron jama’a ba.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce abin ya faɗo ba zato ba Tsammani.

Sai dai Majiyar AIT ta tabbatar da Cewa Amurka ce ta fara aiwatar da kudirinta a Najeriya na kai hare-hare inda take zargin Akwai Ƴan Ta'adda.

Babbar Ayar Tambbayar wannan hari zai zama kuskure ko Ganganci ? Duba da cewa karon farko da fatawa an sami akasin kai hari Yankunan Musulmi.

Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!!!Allah Ya yi wa ɗaya daga cikin jaruman shirin mu na Labarina Series wato Jidda Muh...
25/12/2025

Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!!!

Allah Ya yi wa ɗaya daga cikin jaruman shirin mu na Labarina Series wato Jidda Muhammad Kontagora wadda ke taka rawar Fulani, matar Sarkin Gabas rasuwa.

Jidda, wadda ta dade ta na fama da ciwon Gyambon Ciki wato Ulcer, ta sha fama da jinya a baya-bayan wadda ta shafe kusan watanni 2 ta na kwance ta na jinyar, kamin komawa ga Mahaliccin ta a yammacin wannan rana ta Alhamis, 25 ga watan Disambar shekarar 2025.

Tabbas mun yi babban rashi a wannan kamfani na Saira Movies, la'akari da kasancewar ta ɗaya daga cikin manyan masu taka rawa a shirin Labarina Babi na 3 da mu ke tsaka da haskawa a yanzu haka.

Da fatan Allah Ya jikan ta da rahamarSa. Ya sa aljanna makoma da mu gaba ɗaya. Amin.

Nigerian News

19/12/2025

Drivern Chief of Staff kuma SSA on Domestic To His
Excellency Alh Muhammadu Inuwa Yahaya Tare da Dan
Buba Hon Councilor Shamaki Ward Gombe State lalle APCn

17/12/2025

WANNAN BA DABI'A BACE MAI KYAU

Kamar yadda zaku gani a cikin bidiyo, wani dan Majalisar dokoki ne a jihar Zamfara mutanen gari s**a ci zarafinsa, tare da watsa masa kasa da jifa da duwatsu, aka keta masa suturansa

Wanda ya falla wa dan Majalisar mari a fuskarsa ya fi kowa zama marar mutunci da rashin tarbiyya

Wannan dabi'a da wasu ke yi na jifan Shugabanni ba dabi'ar mutanen kirki bane, idan Shugaba yayi abinda bai dace ba sai abi hanyar da doka ta tanadar wajen hukuntashi, ko a jira lokacin zabe a canza shi da wani

Allah Ya shiryar da mu

BREAKING NEWS ABUJA –THE embattled Chief Executive of the Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authori...
17/12/2025

BREAKING NEWS

ABUJA –THE embattled Chief Executive of the Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority NMDPRA Engr. Farouk Ahmed and his counterpart in the Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission, NUPRC, Gbenga Komolafe, have resigned.

Already, President Bola Tinubu has asked the Senate to approve the nominations of two new chief executives for the NMDPRA and the NUPRC.

A statement by the presidential spokesman, Bayo Onanuga, explained that the President’s requests followed the resignation of the duo.

Both officials were appointed in 2021 by former President Buhari to lead the two regulatory agencies created by the Petroleum Industry Act (PIA).

To fill these positions, President Tinubu has written to the Senate, requesting expedited confirmation of Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan as CEO of NUPRC and Engineer Saidu Aliyu Mohammed as CEO of NMDPRA.

The two nominees are seasoned professionals in the oil and gas industry.

Eyesan, a graduate of Economics from the University of Benin, spent nearly 33 years with the NNPC and its subsidiaries. She retired as Executive Vice President, Upstream (2023–2024), and previously served as Group General Manager, Corporate Planning and Strategy at NNPC from 2019 to 2023.

Engineer Saidu Aliyu Mohammed, born in 1957 in Gombe, graduated from Ahmadu Bello University in 1981 with a Bachelor’s in Chemical Engineering. He was announced today as an independent non-executive director at Seplat Energy.

US President Donald Trump has announced new travel restrictions affecting several African countries, including Nigeria a...
17/12/2025

US President Donald Trump has announced new travel restrictions affecting several African countries, including Nigeria and Tanzania, as part of expanded US entry measures targeting multiple nations worldwide.
Under the policy, Nigerians and Tanzanians applying for US visitor, student, or exchange visas will face partial restrictions. The White House says the decision is based on security concerns, visa overstay data, and gaps in screening and information-sharing. Across Africa, other countries under partial restrictions include Burundi, The Gambia, Malawi, Senegal, Gabon, Zambia, and Zimbabwe. Meanwhile, countries facing a full suspension of entry include Burkina Faso, Niger, Mali, Sierra Leone, South Sudan, Eritrea, Sudan, Republic of Congo, and Somalia.
Notably, several African countries, including Ghana, Kenya, South Africa, Uganda, and Rwanda — are not affected and their citizens remain eligible to travel to the US under existing visa rules.

17/12/2025

NA THIS PERSON PAY $ 5,000,000 allegedly for his children school fees, Alhaji aliko dangote said even himself the king of money for Africa he no go do this madness.
Dangote also said a civil servant should be prosecute about where this kind of money come from because his life time of work as a civil servant Mr faruk cannot get this kind of money.

My question is where is Mr faruk got this kind of money?

Hauka Ko Hankali?Wannan bawan Allah sunan sa Engr Faruk Ahmed,shine shugaban hukumar lura Da albarkatun man fetur guda d...
16/12/2025

Hauka Ko Hankali?
Wannan bawan Allah sunan sa Engr Faruk Ahmed,shine shugaban hukumar lura Da albarkatun man fetur guda daga cikin hukumomin dake karkashin kamfanin man fetur na kasa.
Alhaji Aliko Dangote ya zarge shi da kashewa 'yayan sa dala miliyan biyar a matsayin kudin karatun Sakandare ,a kasashen Turai.
Kamar yadda kuke gani ga sunayen 'ya'yan da makarantun Da suke da Kuma kiyasin kudin da ake biya.

Mutumin nan fa ma'aikacin gwamnati ne wanda ya sami dama Kuma yake damawa.
Koda yake zargi ne, amma wannan abu cin fuska ne ga talakawan Nigeria musamman Arewa domin wannan mutum Dan Sokoto ne,jihar dake cikin jihohin Da dubban yara basa zuwa makaranta saboda talauci.

Kun san yawan dala miliyan biyar kuwa? Kun san makarantu nawa za'a iya ginawa da dala miliyan 5?
Ya Kamata gwamnatin tarayya ta shiga wannan maganar Ko domin talaka ya gane cewar tana yi domin sa, shin idan ka kashe dala miliyan biyar a karatun Sakandare Na yayan ka 4 nawa zaka kashe a karatun su Na jami'a,shin me yasa EFCC ba zata binciki wannan zargi ba,shin Shi Engr Faruk a Ina ya Samo wannan kudi gada yayi daga magabatan sa,Ko kuwa alherin ofis ne?

Duk wadannan amsoshi ne Da yak**ata aji EFCC ta samar Idan Kuma sharri aka yi masa Sai ta bayyana.

Yin hakan shi Zai gamsar Da mu cewar binciken su Abubakar Malami Da su Chris Ngige Na tsakani Da Allah ne, Na siyasa Da bi ta Da kulli ba.

Nasir salisu zango

HARKALLAR BILIYOYIN NAIRA: Yadda Ganduje a ɓoye a musanya mallakin hannun jarin gwamnatin Kano na tashar Dala da wani ka...
29/09/2025

HARKALLAR BILIYOYIN NAIRA: Yadda Ganduje a ɓoye a musanya mallakin hannun jarin gwamnatin Kano na tashar Dala da wani kamfani mallakar ƴaƴansa

Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya tsunduma cikin wata badakalar harkallar biliyoyin naira da ya karkatar zuwa wani kamfani mallakar ƴaƴansa, wanda ya k**ata wannan hannun jari na kaso 20 cikin 100 na gwamnatin jihar Kano ne.

A binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta yi ta gano cewa kason gwamnatin Kano a tashar sauke kaya na Dala Ganduje ya karkatar da kashi 20 cikin 100 na kason gwamnatin Kano zuwa wani kamfani mai zaman kansa wanda mallakin ƴaƴan sa ne k**ar yadda bincike ya nuna.

Kuma an bankado cewa ita wannan harkallar sai da ya saka ‘ya’ƴansa a cikin wannan kamfani tun da farko kafin ya mika wa kamfanin ƴaƴansa wannan kaso, ita jihar kuma sai da ta ji a salansa.

Hakan ya cire Jihar Kano daga zama mai hannun jari a aiki gaba ɗaya, ya kuma sanya ‘ya’yansa su zama daraktoci da masu wannan hannun jari. Haka kuma ba da jimawa ba Ganduje wanda a lokacin sa ne gwamna, ya ba da kwangilar ayyuka da asali gwamnatin jiha ce ke da alhakin aiwatarwa bisa yarjejeniyar da ka kulla tun farko.

Yadda Kano ta samu kaso a tashar sauke kaya ta Dala

A ranar 4 ga Satumba 2006, kusan shekara goma kafin Ganduje ya hau mulki, Gwamnatin Jihar Kano ta sayi kaso 20 cikin 100 a tashar (Dala Inland Dry Port Limited) a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.

Kwamishinan kasuwanci, masana’antu da haɗin gwiwa na Shekarau, Ahmad Yakasai, ya sanya hannu a yarjejeniyar a wancan lokaci.

Wannan mallaka da jihar Kano ta yi a lokacin ya biyo bayan manufar ci gaban tashoshin sauke kaya da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar a shekarar 2003, wadda ta karfafa gwiwar Kamfanoni masu zaman kansu su gina tashoshin, yayin da gwamnatin tarayya da jihohin masaukin tashar za su rika samun kaso kaɗan na hannun jari.

Wannan yarjejeniya ta gindaya cewa masu kamfanoni masu zaman kansu ba za su samu kason da ya wuce 60 cikin 100 ba, yayin da aka ware kaso 20 cikin 100 ga gwamnatin tarayya da wani kason 20 cikin 100 ga gwamnatin jiha.

Har ila yau wannan yarjejeniya ta kuma tanadi cewa gwamnati za ta ba da tashoshin da ta riga ta gina ga kamfanoni masu zaman kansu haya na shekaru 15 zuwa 25, gwargwadon kayan aiki da aka girke. Idan kuma kamfanonin ne s**a gina tashar tun farko, tsarin ta fayyace cewa kaso na gwamnatin tarayya da na jiha zai kasance kalilan ne.

Tashar Sauke kaya ta ‘Dala Inland Dry Port’

Tashar Dala Inland Dry Port na da matukar muhimmancin gaske a Kano, cibiyar kasuwanci ta Arewacin Najeriya. An ƙirƙire ta ne domin sauƙaƙa shigowa da fitar da kaya, rage lokacin jigilar su, da kuma inganta cinikayya da ƙasashen makwabta marasa gabar teku k**ar Nijar, Chadi da Kamaru.

Bisa ga wasu muhimmin takardu da PREMIUM TIMES ta mallaka, Jihar Kano ta ɗauki alhakin biyan kaso 20 cikin 100 na hannun jarinta ta hanyar samar da ababen more rayuwa, wato hanyoyi, shinge, wutar lantarki da ruwa a wurin aikin Zawachiki da ke karamar hukumar Kumbotso ta jihar.

Sai dai, tsohon gwamna Shekarau, wanda ya yi wa’adin mulki biyu a jere daga 2003 zuwa 2011, bai aiwatar da wani aiki ba a tashar.

Haka shima magajinsa, Rabiu Kwankwaso, wanda wa’adinsa na biyu da ba a jere ba ya ƙare a 2015, shi ma bai waiwayi tashar ba kwatakwata.

PREMIUM TIMES ta gano cewa, bayan Ganduje a lokacin ya na gwamna, saka ‘ya’yansa a cikin kamfanin da za su mallaki wannan tasha, sai ya zaftari kudin jihar sar sama da naira biliyan 2 ya bada kwangilar a gyara wanna tasa domin ta soma aiki. Yayi amfani da ikonsa na gwamna a wancan lokacin in da ya yi gaban kasa ya maika kason jihar ba tare da bin doka da ka’ida ba zuwa ga wannan kamfani da ya’yansa ke da mallaki.

Babban darektan ma’akatar kasuwanci da cinikayya ta jihar Kano Bashir Uba, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa lallai jihar Kano bata saida wa kowa hannun jarinta na tashar dala ba. Hasali ma a yanzu haka ta binciken yadda aka yi wasu da ba gwamnati ba ke da mallakin kashi 80 na hannun jarin wannan tasha.

” Gwamnatin Kano ta na shirin kara jarinta a wannan tasha, amma kuma dole za ta gudanar da bincike kan badakalar da ya cukuikuye masu mallakar wannan tasha a yanzu.

PREMIUM TIMES ta ziyarci wannan tasha ta iske ana tafka hadahada ta kasuwanci matuka, sai dai kuma ga yadda lamarin yake jihar Kano bata mafana da komai a wannan tasha.

19/09/2025

Nigerian news is back

Address

Madalla
Abuja
910101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nigerian News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category