18/10/2022
YANZU-YANZU: Ana zargin Shugaban Jam'iyyar APC, Adamu Da Karbar Cin Hanci Domin Yiwa Jam’iyyar Zagon Kasa
Wasu masu zanga-zanga a ranar Talata sun mamaye sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, inda s**a dakile gudanar da dukkan ayyuka
Daga cikin masu zanga-zangar sun zargi Adamu da karbar cin hanci daga wasu ‘yan siyasa a jam’iyyar PDP a babban birnin tarayya Abuja, domin tabbatar da cewa jam’iyyar adawa ta lashe zaben FCT a 2023.
A yayin zanga zangar an bijirewa duk wani kiraye-kirayen da jami’an tsaro s**a yi, inda s**a bukaci a gaggauta tsige shugaban jam’iyyar Abuja, Abdulmalik Usman, inji rahoton Daily Sun.
“Dole ne a tabbatar da cewa ba a rantsar da Abdulmalik a karo na uku ba, idan har shugaban jam'iyya na kasa ya kasa hakan na nufin ya karbi kudi daga hannun PDP domin APC tai rashin nasara a babban birnin tarayya Abuja a zaben 2023,” inji wasu daga cikin masu zanga-zangar