25/09/2026
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya halicce mu kabilu da harsuna daban-daban domin mu san juna, ba domin mu tozarta juna ba. Idan muka duba tarihin kasar nan tamu, musamman Arewa, zamu ga cewa mu bishiya ce guda daya. Amma wajibi ne mu tambayi kanmu: Wanene ya raba mu, har iskar rarrabuwa take neman karya mu?
1. Tsarin Turawa: Tushen Durkushewar Mu
Ya kamata mu gane cewa, babban makamin da Turawa s**a yi amfani da shi ba bindiga ba ne, face Tsarin Rayuwa da s**a dasa mana wanda ya sabawa asalinmu. Sun zo da dabarar raba kawunan musulmai, s**a ja iyakokin da s**a raba Katsina da Maradi, s**a mayar da mu masu kyamar juna ta hanyar dasa kabilanci a zukatanmu.
Babban kuskuren shine Sun sa mu jin kunyar harshenmu da asalinmu, muka koma muna tinkaho da tsarin da aka gina domin a mulke mu, maimakon tsarin da Allah Ya saukar domin ya 'yanta mu.
"Tsarin Turawa tamkar wata sarkakiya ce; duk kyanta, ba ta kai ga 'yanci ba, sai dai kawai ta kai ka ga biyayya ga wanda ya kera ta."
2. Addini da Harshe: Ma'ajin Kimiyya ta Gaskiya
Kafin Turawa su san yadda ake rubutu ko lissafi, Musulunci ya riga ya haska duniya da wani irin haske na musamman. Ya kamata matasanmu su sani:
Duk wata kimiyya da ake tinkaho da ita yau, tushenta yana cikin Alkur'ani da hadisan Manzon Allah (SAW) da binciken magabatanmu.
Muddin muka ci gaba da amfani da Harshen Turawa da tsarin tunaninsu wajen neman ci gaba, zamu dauka cewa su ne iyakar ilimi, alhali kuwa a cikin harshenmu da addininmu ne dukkan mu'ujizozin duniya suke a boye.
3. Najeriya: Kalubalenmu a Yau
Abin bakin ciki ne yau kaga musulmi yana kyamar musulmi dan uwansa saboda Fahimta Wannan shi ne babban nasarar da Turawa s**a samu a kanmu; sun bar mana kabilanci domin mu shagala da juna yayin da suke ci gaba da ruguza tarbiyyarmu. Gidajenmu sun cika da 'yan gudun hijira saboda mun saki asalinmu, mun bi tsarin mulkin da ba namu ba wanda ba shi da adalci a cikinsa.
Lokaci ya yi da zamu kakkabe duk wani tsari na asalin makiyan mu