Tudun Jae online TV

Tudun Jae online TV *Journalist
*Content Creator

25/06/2025

JIBWIS NHQT JOS (GWAGWALADA BRANCH) ZATA GABATAR DA WA'AZIN GORON SALLAH A GIRI GAUTA 25/06/2025.
ZAMUYI LIVE IN SHA ALLAH 8pm

Shin kun san waye ya rikewa Dr Ahmad Gumi Abin magana? Idan kun sani ku rubuta mana Sunan shi A Comments section.Tudun J...
24/06/2025

Shin kun san waye ya rikewa Dr Ahmad Gumi Abin magana? Idan kun sani ku rubuta mana Sunan shi A Comments section.

Tudun Jae online TV

Zuwa ga ofishin kodinetan gasar karatun Alqur'ani na JIBWIS (NHQ Jos)Ba zamu gajiya ba, muna ƙara tura ƙoƙon bara zuwa o...
24/06/2025

Zuwa ga ofishin kodinetan gasar karatun Alqur'ani na JIBWIS (NHQ Jos)

Ba zamu gajiya ba, muna ƙara tura ƙoƙon bara zuwa ofishin kodinetan gasar karatun Alqur'ani mai girma na ƙungiyar Izala kan sake nazarin dawo da izu 60 kamil k**ar yanda mutane suke ta bayar da shawara. Rashin shi matsala ne babba. Babban hadafin Musabaqa shine zaburar da matasa kan haddan Alqur'ani da iya karanta shi, ma'anar sa, da kuma riwayoyin sa.

Ɗan takaran izu 40 wanda bai san komai dangane da Qira'at ba, da wuya ya iya tsallakawa kai tsaye zuwa izu 60 da ruwayoyi 5 cikin shekara ɗaya. Sai dai in dama yana da ido a kai, ko kuma ya zamo ɗan baiwa. Duk da sanda mutum ya kammala haddar sa, akwai buƙatar muraja'a ta musamman. Sannan ita kan ta riwayaat tana buƙatar sai mutum ya kyautata muraja'ar sa kafun ya tsunduma cikin ta. Hakan ya saka wasu da yawa suna ajiye Musabaqa a hizifi 40. Da yawa sun ji a ran su ba zasu iya ba. Ina ga ci baya aka samu ga wanda yake da izu 40 ya kasa ƙarasa haddan izu 60, ko kuma ya haddace amma bai da muraja'ar ta mai kyau.

Bugu da ƙari, rashin izu 60 kamil ya saka an samu cunkoso a izu 40. Waɗanda ya k**ata su yi izu 60 sun tsaya a izu 40 sun danne masu tasowa. Wasu waɗanda a baya suke izu 60 ma sun dawo izu 40. Sannan za'a samu yawan maimaitawa. Mutum zai ta maimaita izu 40 duk shekara, har dai ba wai yaje national yayi na ɗaya ba ne.

Tsallakawa daga izu 40 zuwa izu da riwayoyi 5, musamman ma cikin su akwai Khalaf da Warsh, k**ar tsallakawa ne daga izu 4 zuwa izu 60. Wannan shine ƙaramin misali.

Muna roƙon ya zamo akwai izu 60 kamil k**ar yanda ake yi a baya, sai kuma izu 60 da riwayoyi. Daga izu 60 mutum zai fi sauƙin tsallakawa zuwa riwayoyi. Sannan ko bai tsallaka ba, aƙalla ya samu hadda cikekkeya da muraja'ar ta sanadin Musabaqa saɓanin in a izu 40 ya tsaya.

Follow Tudun Jae online TV
Ahmad Muhammad Gambo ✍️

Boom💥💥💥Ƙasar Saudiyya:Saudiyya ta bayyana "matuƙar damuwa" game da harin da Amurka ta kai a cibiyoyin ƙera mak**an nukil...
22/06/2025

Boom💥💥💥Ƙasar Saudiyya:

Saudiyya ta bayyana "matuƙar damuwa" game da harin da Amurka ta kai a cibiyoyin ƙera mak**an nukiliya na Iran sannan ta yi kira ga ƙasashen duniya su ƙara ƙaimi wajen samun mafita ta siyasa a wannan rikici.

Kuyi following Tudun Jae online TV domin samun ingantattun labarai

Gaskiya Ya Zama Dole a Yabawa Mataimaki Na Biyu Sheikh Dalha Da Kuma Sheikh Ibrahim Duguri.Wato Ba Karamin Gudunmawa S**...
20/06/2025

Gaskiya Ya Zama Dole a Yabawa Mataimaki Na Biyu Sheikh Dalha Da Kuma Sheikh Ibrahim Duguri.

Wato Ba Karamin Gudunmawa S**a Bawa Alhazai a Wajen Aikin Hajji Ba, Abune Mai Kyau Mu Dinga Yabawa Malan Mu Idan Sunyi Aikin Alkairi Irin Wannan.

Allah Ya Kara Taimakon Ku Ya Daura Ku Akan Dai Tareda Sauran Maluma Baki Daya.

Tudun Jae online TV follow and share

ya

JUST IN 💥 Former Vice President His Excellency Namadi Sambo Dumps PDP Joins APC.Tudun Jae online TV follow for more upda...
18/06/2025

JUST IN 💥

Former Vice President His Excellency Namadi Sambo Dumps PDP Joins APC.

Tudun Jae online TV follow for more updates

SHUGABAN JIBWIS NA ƘASA :sheikh Naseer Abdulmuhyee Shugaban majlisar gudanarwa na Kasa na JIBWSI NHQ JOS.daga kasar Makk...
17/06/2025

SHUGABAN JIBWIS NA ƘASA :sheikh Naseer Abdulmuhyee Shugaban majlisar gudanarwa na Kasa na JIBWSI NHQ JOS.daga kasar Makkah yayin wata ziyara ta Musamman daya gabatar a jiya tare da 'yan tawagar shi muna addu'ah Allah yasanya wa ziyarar albarkha da alheri amin.

Tudun Jae online TV
Hoto da Labari : Sadiq Amsy

BALA'IN DA ZAI FARU IDAN AKA HARBA MAKAMIN NUCLEAR! 💣📌 Saboda sanin mugun hatsarin makamin nuclear ne ya sa manyan kasas...
14/06/2025

BALA'IN DA ZAI FARU IDAN AKA HARBA MAKAMIN NUCLEAR! 💣

📌 Saboda sanin mugun hatsarin makamin nuclear ne ya sa manyan kasashe suke rikicewa idan s**a ji labarin wata kasa tana kokarin mallakarsa, saboda lamarin ba na wasa ba ne.

Sannan mafi yawancinmu kawai muna jin sunan nuclear ne amma ba lallai ba ne idan mun san irin hatsarinsa, bari ka ji dalilin da ya sa Malam Bahaushe ya kira shi da sunan “makamin kare dangi” a wanann misalin da zan bayar na bala'in da zai faru idan aka harba shi.

Misali, gobe Lahadi da asuba, sai Russia (tana da nuclear warheads guda 5,500+), sai ta harba guda daya ga birnin TaAbib, ga abun da zai faru cikin 1-second:

—Nuclear bomb din zai haskaka samarin samaniya fiye da hasken rana

—Nan take duk wanda ya kalli hasken nan zai makance

—Surface temperature na wajen zai haura 10,000°C (duk zafin da ake yi a Sokoto/Maid ba ya wuce 46°C, imagine 10,000 now!)

—Kusan duk wani abu mai rai zai mutu nan take (lamarin da zai kashe mutane sama da 1,000,000)

—Duwatsu, karafuna, bishiyoyi, gine-gine... duk za su fara tafarfasa

—Duk wani gini (ko ya kai Burj Khalifa tsayi) nan take zai rushe
..wannan a cikin 1-second kenan fa.

Bari mu ci gaba. A cikin 1-minute kuma ga abun da zai faru:

—Duk wani flammable abu k**ar oil, gas stations, chemicals da sauransu za su k**a da wuta

—Sannan su ma ababen hawa, da gidaje, da komai da komai za su k**a da wuta

—Mushroom cloud zai tashi har tsayin 20km zuwa sama, sannan ya dawo da gurbatacciyar iska mai dauke da radiation a siffar kura ko hazo
..bari mu sake ganin me zai faru bayan haka:

—Kasar garin za ta lalace k**ar girgizar kasa

—Wadanda s**a yi saura ba su mutu ba za su fara rashin lafiya k**ar cancer, severe injury, amai da gudawa, da sauransu saboda tsananin radiation

—Za a yi tsananin rashin abinci, wuta, da ruwa saboda gabadaya iskar garin da kauyukansa ta gurbace. Wadanda s**a rage ba su mutu ba za su koma k**ar wasu zombies, sai mutuwa ko ina

Bayan duk wadannan kadan daga cikin abubuwan da za su iya faruwa cikin 24-hours kacal, daga nan kuma mutane da dama ba za su kara haihuwa ba (saboda cututtuka ko gurbacewar DNA), wasu ma ko wata daya ba za su kara yi ba.

Gabadaya birnin zai tashi a aiki. Ba zai zaunu ba, ba za a sha ruwan wajen ba, ba za a yi noma ba, sannan iskar da take kadawa a wajen zuwa wasu wurare su ma abun zai shafe su. Wanann lamari zai ci gaba da wakana har na tsawon watakila shekaru 50 zuwa 70. Climate change activists sai dai ku yi hakuri saboda an jika muku aiki!

Nuclear weapon kala-kala ne. Ga misali da karfinsa:

1 — Hiroshima Bomb - wanda ya kashe mutane 140,000+ a 1945 (wannan tsohon version ne) - nauyinsa ya kai 15 kilotons

2 — Modern Bomb - zai iya shafe New York ko Paris duka, nauyinsa ya kai 1,000+ kilotons

3 — Hydrogen Bomb - zai iya shafe kasa sukutum ko kasashe biyu ko uku, kai har yanki sukutum ya kan iya shafewa a doron kasa - nauyinsa ya kai 50,000+ kilotons - shi ne irin wanda Russia ta yi test a 1961 mai suna Tsar Bomba.

Misalin da na bayar a sama shi ne idan aka harba Modern Bomb. Tun da aka fara amfani da nuclear bomb, sau biyu aka taba harba shi kai-tsaye kan mutane, wato na Hiroshima da Nagasaki a 1945 wanda US ta yi.

Yanzu kun ga dalilin Malam Bahaushe na cewa makamin kare dangi ko?

Kafin in rufe ga jerin kasashen da suke da nuclear da adadinsu:

-Russia - 5,889
-US - 5,244
-China - 500
-France - 290
-UK - 225
-Pakistan - 170
-India - 164
-Israel - 90
-North Korea - 40

Allah Ya kiyaye. Kun ga kenan idan za a yi ta harba su k**ar yadda ake harba missiles, ai za a yi wa duniya “reset all” kafin lokacin tashinta ya yi. Amma tabbas Dan-Adam ya kirkiro mugun makami a duniya.

Idan ka fahimta ka yi sharing ga wasu ↗️

✍️ Muhammad Auwal Ahmad ( )
Technologist and Scientist

Rawaitowar : Tudun Jae online TV follow

14th May 2025

13/06/2025

JUMA'AH MUBARAK:Karatun Alqur'ani Mai Girma daga Gwarzo Ahmad Muhammad Gambo




Follow Tudun Jae online TV

Mafificiyar Yini Wacce Rana take fitowa cikinta itace Ranar Juma'a1⃣A Ranar Aka halicci Annabi Adam2⃣A Ranar aka shigar ...
13/06/2025

Mafificiyar Yini Wacce Rana take fitowa cikinta itace Ranar Juma'a

1⃣A Ranar Aka halicci Annabi Adam
2⃣A Ranar aka shigar dashi Aljannah
3⃣A Ranar aka fitar dashi daga ciki

Kuma bazata tsaya ba Sai a wannan Ranar.

Mubarak
Follow Tudun Jae online TV

✍️ Hafiz Nafiu Usman Ibrahim

Address

Gwagwalada

Telephone

+2349161301163

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tudun Jae online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Tudun Jae online TV:

Share

Category