AT-Tablig Wal Irshad 313 Foundation

AT-Tablig Wal Irshad 313 Foundation For Preaching And Propagating The Knowledge Of Ahlulbait (As)

28 ga Watan Muharram :🖤    Ranar Shahadar Sahabi Huzaifa Bin Al-Yamani ,Sahabi Huzaifa bin Yamani Babban Sahabi ne na Im...
13/07/2026

28 ga Watan Muharram :🖤

Ranar Shahadar Sahabi Huzaifa Bin Al-Yamani ,

Sahabi Huzaifa bin Yamani Babban Sahabi ne na Imam Ali (As) sannan yana daga cikin Mutane 7 da s**ayi Sallah Ga Sayyida Zahra (As) bayan Wafatinta!

Ana Kiran Sahabi Huzaifa da Sahibu Sirrin Rasulilillah (S) saboda Annabi Ya Sanar dashi Sunayen Munafukai a Cikin Sahabbai.

Wanda Har Ya Kasance Sahabi Huzaifa Baya Halartar Jana'izar Wasu daga cikin Sahabbai Saboda Kasancewarsu Munafukai da Annabi Ya Sanar dashi Sunayensu.

Amincin Allah Ya Tabbata A Gareka.

Muna Taya Yan uwa Juyayin Wannan Ranar.



https://t.me/Al_irshad313Foundation

25 ga Watan Muharram :🖤    Ranar Shahadar Imam Aliyu Zainul Abidin (As) , Wanda Akewa Lakabi da Al Sajjad (As) .  Aminci...
10/07/2026

25 ga Watan Muharram :🖤

Ranar Shahadar Imam Aliyu Zainul Abidin (As) , Wanda Akewa Lakabi da Al Sajjad (As) . Amincin Allah Ya Tabbata A Gareka Imami Mazlumi.

Muna Taya Yan uwa Juyayin Wannan Ranar.



https://t.me/Al_irshad313Foundation

Eidul Ghadir wannan wanne Eidi ne!!A Ranar goma Sha takwas (18) ga Watan zhul hijjah a Irin wannan Ranar ne manzon Allah...
04/06/2026

Eidul Ghadir wannan wanne Eidi ne!!

A Ranar goma Sha takwas (18) ga Watan zhul hijjah a Irin wannan Ranar ne manzon Allah Muhammad bin Abdullahi ya nasabta Dan uwansa Kuma sirikin sa Imamu Ali a matsayin magajin sa (Khalifansa) a bayansa.

Saboda haka a Irin wannan Ranar Al'ummar musulmi musamman ma'abota wulaya ga ahlul baiti suke bukukuwa da Murna da wannan babbar Rana,Kuma suke isar da wannan babban sako ga Al'ummar musulmi Domin su san abunda manzon Allah ya bar musu ko Babu komai Allah Yana fadi a cikin Alqur'ani cewa:-

وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَىٰ تَنْفَعُ الْمُؤْمِنِينَ
(الذاريات 55:51)

Dan haka yaku Al'ummar musulmi kusani cewa manzon Allah ya bar mana wasiya akan mubi Imamu Ali (as) Domin manzon Allah baibar Al'ummar sa Kara zubeba lallai Allah ya umarci manzon Allah ya Sanya Ali a matsayin Khalifansa kamar yadda yazo a ayar Alqur'ani cewa:-

يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ مِنْ رَبِّكَ ۖ وَإِنْ لَمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ ۚ وَاللَّهُ يَعْصِمُكَ مِنَ النَّاسِ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ

(المائدة 67:5)

Wannan ayar ta sauka ne akan maganar wannan Babban Eidi na Ghadir.

Don Haka Wannan mu'assar ta Al-irshad da dukkan mambobin ta Muna Kara tunatar da Al'ummar musulmi game da wannan babbar Rana wacce Bata da tamka a musulunci domin haka kada mu manta da aiyukan wannan Ranar Domin ribatuwa da ladan Dake tattare dasu.





https://t.me/+n4ZdwJpSjbc2MjA6

Ayyukan Daren Arfa:1- Akwai karanta addu'ar Daren Arfa, addu'a mai tsayi da ke farawa da اَللّـهُمَّ يا شاهِدَ كُلِّ نَج...
25/05/2026

Ayyukan Daren Arfa:

1- Akwai karanta addu'ar Daren Arfa, addu'a mai tsayi da ke farawa da اَللّـهُمَّ يا شاهِدَ كُلِّ نَجْوى. Ana iya dubawa a Mufatihu ko sauran littafan addu'oi.

2- An so karanta Tasbihin da aka ruwaito ana yinsu a ranar Arfa sau dubu.

3- An so karanta addu'ar اَللّـهُمَّ مَنْ تَعَبَّأَ وَتَهَيَّأَ, wacce ita ma tana nan a babin ayyukan daren Juma'a a Mufatihu.

4- Sai Ziyarar Imam Husaini (AS) a Karbala, ko karantawa daga inda ya sauwaka.



https://whatsapp.com/channel/0029VbCvDmfFXUufms6fGC3m

Cikin irin wannan yinin ranar Tarwiyya 8 ga Haj-hajji shekara ta 60 bayan Hijirar Kakansa , Imam Husaini (AS) ya samu la...
25/05/2026

Cikin irin wannan yinin ranar Tarwiyya 8 ga Haj-hajji shekara ta 60 bayan Hijirar Kakansa , Imam Husaini (AS) ya samu labarin cewa Yazidu La'ananne ya ba da umurni kan a fillo masa kansa ko da yana manne da labulen Ka'aba. Don kiyaye alfarmar Dakin Allah Mai Girma, Imam haka ya fita daga Ka'abar, ya bar Makkah, ya nufi Kufa, wanda a hanyarsa s**a tsare shi a Karbala s**a Shahadantar

Ya Laitana Kunna Ma’akum Ya Maulay😭



https://whatsapp.com/channel/0029VbCvDmfFXUufms6fGC3m

Azumin Gobe 8 Ga ZulhijjaGobe Litinin 8 ga watan Zulhijja 1447, Ya dace da Ranar Tarwiyya. Azumi a cikinsa Mustahabi ne,...
24/05/2026

Azumin Gobe 8 Ga Zulhijja

Gobe Litinin 8 ga watan Zulhijja 1447, Ya dace da Ranar Tarwiyya. Azumi a cikinsa Mustahabi ne, kuma wanda ya yi yana da ladan Kaffaran Zunuban shekara 60. Haka kuma, Mustahabi ne yin wanka a cikinsa.



https://t.me/+n4ZdwJpSjbc2MjA6

29 Ga Watan Zulqada.Ranar Shahadar Imam Muhammad Jawad (As). Limami Na 9 Cikin Limaman Shiriya 12 da Manzon Allah (S) Ya...
17/05/2026

29 Ga Watan Zulqada.

Ranar Shahadar Imam Muhammad Jawad (As). Limami Na 9 Cikin Limaman Shiriya 12 da Manzon Allah (S) Ya bar Mana Su a Bayansa.

Yayi Shahada a shekara ta 220 bayan Hijira. Makwancinsa Yana Baghdad Khazimiyya.

🏴السلام عليكَ يا جواد الأئمة



https://t.me/Al_irshad313Foundation

Imam Sadiq (As) Yace:"Allah kaji ƙan Mutanen da s**a kasance Fitulu masu haskawa, Sun kasance masu kira zuwa gare mu da ...
15/05/2026

Imam Sadiq (As) Yace:"Allah kaji ƙan Mutanen da s**a kasance Fitulu masu haskawa, Sun kasance masu kira zuwa gare mu da Ayyukansu da Jajircewar su, ba kamar wadanda suke watsa da Sirrukanmu ba" .

رَحِمَ اللهُ قوماً كانوا سراجاً ومناراً، كانوا دعاةً إلينا بأعمالهم ومجهودِ طاقتِهم، ليس كَمَن يُذيع أسرارنا

📚Tuhaf al-‘Uqul, p. 301



https://t.me/Al_irshad313Foundation

11 Ga Zulqada:❤️Muna Taya Dukkan Muminai Murna da Ranar Haihuwar Imam Ali Bin Musar Ridha (AS).  Limami na 8 a jerin Ima...
29/04/2026

11 Ga Zulqada:❤️

Muna Taya Dukkan Muminai Murna da Ranar Haihuwar Imam Ali Bin Musar Ridha (AS).
Limami na 8 a jerin Imaman Shiriya, halifofin Manzon Allah (S) 12 da ya bar mana a bayansa.

Amincin Allah Su kara Tabbata a gare shi. 🌹💕



https://t.me/Al_irshad313Foundation

7 ga Ramadan 🖤A irin wannan Ranar 7 ga Watan Ramadan kamar yadda yazo a wata ruwaya cewa Sayyiduna Abu Dalib Yayi Wafati...
24/02/2026

7 ga Ramadan 🖤

A irin wannan Ranar 7 ga Watan Ramadan kamar yadda yazo a wata ruwaya cewa Sayyiduna Abu Dalib Yayi Wafati a shekara ta 10 bayan Aiko Manzon Rahama (S) da Sakon Manzanci.

Muna Taya Yan uwa Juyayin Wannan Ranar.🖤




https://t.me/Al_irshad313Foundation

Address

Jos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AT-Tablig Wal Irshad 313 Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category