Tijjaniyya Youth Connect Barikin-ladi Plateau State

  • Home
  • Nigeria
  • Jos
  • Tijjaniyya Youth Connect Barikin-ladi Plateau State

Tijjaniyya Youth Connect Barikin-ladi Plateau State Islam Activities

17/07/2023

Da farko za a ce maka Kitabu Was Sunnah, idan ka yarda sai a ce maka "akan fahimtar magabata", sai kuma a ware maka wasu magabatan a ce su kadai ne na kwarai; daga baya za ka gane ashe ba wani Kitabu Was Sunnah, kawai ra'ayoyin Ibn Taimiyya ake so ka bi sai kuma Albany da zai dinga inganta maka hadisai.

17/07/2023

Asalin komi halas ne. Sai wanda aka haramta…

Komi da komi asalinsa HALAL ne sai wanda Allah ya haramta. Ko Annabi

الأصل في الأشياء الإباحة

Karatun kenan a wurin Mallamai.

17/07/2023

Dr Ahmad Tijjani Al'azhari ne yace ya gano kuskuren Nahawu kusan guda 60 a cikin littafin da Dr Sani ya rubuta yana s**an Sheikh Ibrahim Inyass!

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: "Mafi Alkhairi daga cikin mutane shine wanda Rayuwarsa tayi tsayi Aikinsa ya kya...
14/07/2023

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: "Mafi Alkhairi daga cikin mutane shine wanda Rayuwarsa tayi tsayi Aikinsa ya kyautata"

Kadan daga Cikin Darasin dake Cikin Wannan Hadisin....

Yana da kyau mutum ya yawaita Aikin Alkhairi domin samun tsira da ku6uta Agurin Allah Ranar gobe kiyama.

Yana da kyau mutum yayi amfani da damarsa kafin mutuwa ta Riskesa.

Yana da kyau mutum yasan Duk Alkhairan da ya Aikata Allah zai basa ladansu, haka ma sharri zai sami zunubi.

Allah Yasa Mudace Duniya Da Qiyama Bijahi Sallallahu Alaihi Wasallam 🥰 Amin Ya Hayyu Ya Qayyum 🤲

14/07/2023

Alhamdulillah.

YAN NIGERIANE KE NEMAN YAFIYAR KA BABA.Irin wannan sako na da matukar taba zuciya, da bude Facebook dina yanzu "sai nake...
13/07/2023

YAN NIGERIANE KE NEMAN YAFIYAR KA BABA.

Irin wannan sako na da matukar taba zuciya, da bude Facebook dina yanzu "sai nake cin karo da rubutun Sayyadi Daha Azhary ya ruwauto Maulana Sheikh na cewa " Ya yafe wa dukkan Mutanen Najeriya, yanemi Kowa ya yafe masa shima, albarkan Alqur'ani Maigirma.

Sai na lura da cewa wannan zance ya fito ne a harshen karamci irin na waliyyan ALLAH, amma shi kam bai aikatawa Dan Nigeria kowanne irin laifi ba, bal dai 'Yan Nigeria su ne su kai masa laifi.

DUK WANDA YA KI SHI KO YA ZAGE SHI, BAI KISHI SABODA YA KARBE MASA WATA HAJA BA, BAI KISHI SABODA YA ZALINCESA BA, BAI KISHI SABODA YA MUNANTA MASA MU'AMALA BA, LAIFINSA SHINE "Ya Tallata masa ababen da idan ya rayu akan kiyaye lazimtarsu, to zai amfani lokacinsa, a lahira ba zai kasance cikin nadama ba, wadanda sune:

1- Istigfari.
2- Salati
3- Hailala.

SABODA HAKA, SHI SHEHU BAI DA MAKIYI A ZATIN KANSA, SAI DAI WANDA YA KIRKIRAWA KANSA KIYAYYARSA.

MU YAN NIGERIA MUNA GODIYA DA WANNAN YAFIYA DA MAULANA SHEIKH YAYI MANA, HAKIKA IDAN MUKA DUBA GIRMAN SHA'ANINSA, MUKA DUBA KARANCIN HIDIMARMU GARESHI, TO SAI MU GANE LALLAI YAYI MANA BABBAN GATA DA YA YAFE MANA.

BABA DUNIYAR MUSULUNCI BAZATA TABA MANTAWA DA KAI BA, DOMIN KAYI AIKI TUKURU WANDA YA KEREWA HIMMAR DUBBAI, ALLAH YA KARA TSAWAITA MAKA KWANA, YA KIYAYE MANA LAFIYARKA.

ALHAMDULILLAH.

Dama Malam Sani Rijiya Lemu bai rubuta littafin nan ba, daya huta ma kanshi, gashi ya rubuta ya kuma riga ya sake shi Ma...
13/07/2023

Dama Malam Sani Rijiya Lemu bai rubuta littafin nan ba, daya huta ma kanshi, gashi ya rubuta ya kuma riga ya sake shi Malamai da ɗaliban ilimi sunyi sauri sun tarbe shi sai saukale shi sukeyi dai-dai gwar-gwado.

Na rantse da Allah gazawarsa ta fito fili ƙara-ƙara baida fahimta ko ɗaya a fannin abinda ya rubuta littafin yayi niyyar yin raddi saboda manufar tozarci ga bayin Allah sai gashi ya harɗe kanshi da kanshi ya kuma bayyana ma duniya inda bashi da wayau, ya ƙwafo raddin ɗaya daga cikin malaman da s**a gabata, baisan yayi sara akan gaɓa ba.

Da ace yabi shawarar Ibnu Taimiyya wacce ya bada a cikin littafinsa na Majmoo'al fatawa a Juzu'i na 5 shafi na 29 da shafi na 331 wanda na kawo shi ɗazu anan shafina.

Da yabi shawarar Ibnu Taimiyyah daya zauna lafiya amma saboda azar ɓaɓi da tsautsayi ga inda ya tsinci kanshi nan mafi yawan waɗanda s**aci karo da raddin da akayi masa sunsan ko yanzu ya fahimci ya tafka kuskure.

NB: Zuwa ga masoyansa da kuma ɗalibansa ni ko mu bamuce malaminku ba malami bane, tabbasa malami ne, cikakke na faɗa aji amma a ɓangaren salafawa sannan dan yanada tarin ilimi ba komai ya sani ba, da ace ya yadda da hakan ya tsaya iya matsayinsa kuma iya littattafan salafawa waɗanda anan yafi wayau da asirinshi rufe kamar yadda Ibnu Taimiyya ya faɗa cewa: duk wanda yaje gidan sufaye sai ya dawo yana taɓaɓɓe kuma gashi nan mun gani.

Imam Anas

Baki yakan rasa me zai furta akan Maulana Sheikh (R.A)  sai dai ayi kurum Allah ya kara inganta maka lafiya da jinkiri m...
13/07/2023

Baki yakan rasa me zai furta akan Maulana Sheikh (R.A) sai dai ayi kurum Allah ya kara inganta maka lafiya da jinkiri me amfani

Saqon da ya fito yau ya karamun imani da yakini akan Wiliyarku da kusancinku da Allah Maulana (R.A)

ka mana komai wallahi babu abunda ya rage da baka manaba, tsakanin mu da kai sai dai mu nemi yafiyarku..

Astagfirullah🙏🙏🙏

13/07/2023

Mushiriki Biɗar Taimako da Agaji Yake Agun Shuwagabannin Izala Su saka Baki A sakoshi Ya Manta Allah.

YANZU-YANZU: Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA Ya Bayyana Cewa Yana Bukatan Kowa Ya Yafe Masa Albarkacin Alkur'a...
13/07/2023

YANZU-YANZU: Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA Ya Bayyana Cewa Yana Bukatan Kowa Ya Yafe Masa Albarkacin Alkur'ani Mai Girma, Shima Ya Yafe Wa Kowa.

Shehin Malamin Musulunci Kuma Babban Jagoran Darikar Tijjaniyya A Duniya Ya Bayyana Hakan Ne A Birnin Tarayya Abuja Yau Alhamis 13/07/2023.

Allah Ya Kara Wa Maulana Sheikh Dahiru Lafiya Da Nisan Kwana Albarkacin Annabi ﷺ. Amiin

Tijjaniyya Media News

Address

Plateau State Barikin Ladi Local Government Area
Jos

Telephone

+2348059628303

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tijjaniyya Youth Connect Barikin-ladi Plateau State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Tijjaniyya Youth Connect Barikin-ladi Plateau State:

Share

Category