03/10/2026
❤️🌹 KALAMAN SOYAYYA 🌹❤️
Da ace zuciyata tana iya magana, da ba ta gajiya da furta sunanka. Domin tun daga ranar da ka samu wuri a cikinta, komai ya fara samun wani sabon ma’ana.
Ba wai ina son kasancewarka a rayuwata kawai nake so ba… ina son ranar da zan kalli idonka, in ji cewa duk tsawon jiran da na yi, bai tafi a banza ba. 🥹❤️
Wasu mutane suna shigowa rayuwarmu su wuce kamar baƙi, amma akwai waɗanda idan sun zo, zuciya ta ce: “Wannan shi ne wanda nake so ya zauna.” ❤️🌹
Idan soyayya ita ce kuskure, to ina roƙon Allah kada Ya gyara min wannan kuskuren. 🥰❤️