23/02/2026
Kungiyar Muryar direbobi da mamallaka baburan Adaidaita sahu ta jihar Kano, VOTORA, ta nuna goyan bayanta ga shirin gwamnatin Kano na sanya wa ababan hawa na’urar tracker.
Shugaban kungiyar ta VOTORA Kwamred Nazifi BK Gidan Kudi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a jihar Kano.
Ya ce sanya nau’rar ta tracker a baburan Adaidaita sahun zai taimaka wajen fitar da ɓata gari daga cikin sana’ar tasu da kuma inganta kariya ga rayuwa da kuma dukiyar al’umma.
Kwamred Gidan Kudi yayi kira ga direbobin Adaidaita sahun da su bawa wannan shirin hadin kai domin a samu nasara a cikinsa.
Kungiyar tace VOTORA tracker ɗin wannan lokacin ta sha bamban da wadda aka gani a gwamnatin da ta gabata kasancewar wannan karon na'ura ce ba takardar ba
📸 Aminu Rimin Kebe